• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Za Ki Magance Tabon Fuska

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Tabon fuska

Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.

A yau shafin namu zai zo muku da yadda za ki magance tabon fuskarki
Idan kina fama da tabon fuska wanda hakan ya faru ne sakamakon mutuwar kuraje da suka fito a fuska, to ki zabi daya daga cikin wadannan hanyoyi don magance tabon fuska:

Na daya: ki kwaba garin bawon lemon zaki da ruwan lemon tsami da ruwa sai ki rika shafawa a kan tabon ya yi kamar minti biyar sai ki wanke.
Na biyu: ki hada tumatur da zuma ki shafa a inda tabon yake, ya yi kamar munti 15 sai ki wanke ki yi hakan kamar sau biyu a sati.
Na uku: Ki kwaba zuma babban cokali daya da babban cokali daya na orange peel powder sai ki shafa a kan tabon sannan ki wanke bayan ya bushe, ki yi hakan kamar sau uku a sati.
Na hudu: Ki shafa ruwan alo bera a kan tabon kullum in za ki kwanta sai ki wanke da safe.
Na biyar: Ki matse lemon tsami sai ki yi amfani da koton ki rinka shafawa a kan tabon ki barshi ya yi minti 10 sai ki wanke, ki yi hakan sau uku a sati.
Na shida: ki nika Dankalin turawa sai ki shafa a inda tabon yake ya yi kamar minti 10 sai ki wanke.
Na bakwai: Ki nika tumatir da kokumbe sai ki tace ki sa a firij ya yi kankara sai ki ringa shafa kankarar a kan tabon kullum.
Kurajen fuska ko pimples a turance
Wasu kuraje ne da suka fi fitowa a fuska musamman idan mutum yana ta’ammali da mayuka iriiri ba tare da kula da man da ya dace da fatar fuskar ba.
Matsalar kurajen fuska tafi shafar mata musamman matasa inda za’a ga wasu matan har nikaf suke sanyawa a fuskokin su saboda kar a ga ta’adin da kurajen suka yi musu a fuska. Maza ma su kan fuskanci irin wannan matsala ta kuraje a fuska.

Kadan daga cikin abubuwan dake janyo kurajen fuska sun hada da:
yawan cin abu mai maiko, amfani da mayukan da basu dace da fatar fuska ba, kwayoyin cuta, shiga rana sosai, aiki cikin zafi.

Mutane da dama kan kashe makudan kudade don sayen maganin da zai magance musu kurajen amma kuma yawanci ba’a samun biyan bukata. Ana iya magance kurajen fuska ta wadannan hanyoyin:

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

Bawon Lemon Zaki:
Ana shafa bawon lemon zaki a inda abin ya shafa sai ki barshi ya kwana da safe sai ki wanke da ruwan dumi.

Zuma:

Za ki samu zuma mai kyau ki goga da auduga a fuska, ki barshi zuwa ‘yan mintuna sai ki wanke. Za ki iya maimaitawa kamar sau biyu a rana har kurajen Su fita.

Ruwan lemon tsami:

Ruwan lemon tsami wata sahihiyar hanya ce mai matukar amfani wajen maganin kurajen fuska. Lemon tsami yana taka rawar gani sosai wajen kashe kananan kwayoyin cuta a fuska da kuma fitar da maikon fuska.

Yadda za ki yi amfani da lemon tsami shi ne

Ki samu lemon tsami ki matse ruwansa sai ki samu auduga mai tsafta ki dinga goge fuska daita kafin ki kwanta bacci, da safe sai ki wanke fuskar da ruwan dumin, za ki iya maimaitawa sau biyu ko uku a rana har kurajen su fita.

Ganyen Darbejiya, Man Darbejiya.

Ana kwaba ganyen Darbejiya da man Darbejiya a shafa a fuska zuwa mintuna biyar sai ki wanke da ruwan dumi ko ki dinga shafa man da auduga a fuskar har zuwa lokacin da kurajen za su baje.

Kurajen fuska dai sun dade suna bata wa mutane fuskokinsu har ta kai wasu ma sun gaji da nema wa kansu magani, mata ma kan yi duk yadda za su yi su rufe fuskokinsu don kar a ga kurajen, wasu ma kan yi amfani da hodar foundation akai-akai don boye kurajen dake fuskarsu. Wannan hanyoyi da na lissafa za su taimaka sosai wajen cire kurajen fuska cikin sauki ba sai mutum ya kashe makudan kudade ba wajen neman magani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Ramadan: Wike Ya Raba Wa Musulmai Kayan Abinci A Abuja

Ramadan: Wike Ya Raba Wa Musulmai Kayan Abinci A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

October 21, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

October 21, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi

October 21, 2025
Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja

Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja

October 21, 2025
Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

October 21, 2025
Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

October 21, 2025
An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.