Manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Ingila, Manchester City da Arsenal sun buga kunnen doki a wasan mako na 30 na gasar Firimiya da suka buga a filin wasa na Etihad Stadium dake birnin Manchester.
An yi tsammanin wasan tsakanin manyan kungiyoyin biyu ya yi zafi duba da cewa dukkansu suna fatan darewa saman teburin Firimiya na bana yayin da ake gab da kammalawa.
Amma kowane bangare ya jajirce domin ganin ya hana abokin karawarsa jefa kwallo ko daya a ragarsa, da hakan kuma Liverpool ta koma matsayi na daya akan teburin gasar bayan ta doke Brighton a Anfield.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp