Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin kamo ‘yan kwangilar da suka fara aiki suka gudu a fadin Jihar Kaduna.
Gwamnan ya ce duk dan kwangilar da ya san tsohuwar gwamnatin jihar karakshin jagorancin, Malam Nasiru elRufai ta ba su aiki gina tituna suka fara ba su gama ba, su gaggauta dawowa bakin aikinsu ko su fuskancin fishin gwamnatin jihar.
- Dambarwar Bashi Ta Dumama Jihar Kaduna
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5, Sun Saki 51 Bayan Biyan Fansa A Kaduna
Sanata Uba Sani, ya yi furucin ne a wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da sarakunan gargajiya da wakilan kungiyar ‘yan kwangilar jihar.
Ya ce, “Ina umarnin duk wani dan kwangilar da ya san ya fara aiki a Jihar Kaduna daga shekaru takwas zuwa yanzu da ya tabbatar ya dawo bakin aikinsa, saboda kudin gwamnatin Jihar Kaduna aka dauka aka ba su aiki. Babu dalilin da zai sa don babu kudi a jihar su kwashe kayansu su gudu, haka nan za su zo su ci gaba da aiki idan an samu kudi a ba su har su gama aikinsu.
“Kwanan baya na kai ziyara garin Zariya, sai na tarar ko’ina an yi maka-makan ramuka an hake ko’ina, kuma babu kayan aikin ‘yan kwangilar, sai na tambaya aka ce wai sun kwashe kayansu sun bar jihar, saboda babu kudi. Ya zama dole su dawo bakin aiki tun da har an dauki kudin gwamnatin jihar an fara biyansu, kuma sun amince sun fara Aiki.
“Ina umartarsu da su gaggauta dawowa bakin aikin domin kammala aikin da suka fara,” in ji shi.
Gwamnan ya bukaci kungiyar ‘yan kwangilar Jihar Kaduna da su kara hakuri gwamnatin jihar tana sane da halin da suke ciki kuma za ta ci gaba da yin aiki da su domin ciyar da Jihar Kaduna gaba.