ABDULLAHI YAKUBU WUNTY, guda ne daga cikin Injiniyoyin Gidan Rediyon Gwamnatin Jihar Bauchi (BRC), wanda Allah ya yi wa baiwar gyaran rediyo tare da iya hada gidan rediyon, ta yadda har yake iya jefa na’urarsa a ji sautin a wasu jihohi da dama na cikin kasar nan. Ya taba hada gidan rediyo mai suna ‘Wunty Rediyo’ a cikin garin Bauchi, a lokacin da yake yada shirye-shiryensa; ana jin sa a ko’ina a fadin jihar har ma da wasu jihohin. Saboda haka, za mu iya cewa, Nijeriya na da masu matukar baiwa; sai dai samun damar baje kolin fasaharsu ta rage. Wakilinmu na Jihar Bauchi, KHALID IDRIS DOYA ya tattauna da shi kamar haka:
Da wa muke tare a yanzu?
Sunana Abdullahi Yakubu Wunty, wanda aka fi sani da Abdullahi Na’ura. An haife ni a cikin garin Bauchi, yanzu haka ina da shekara sama da 53 a duniya. Na fara karatun makarantar firamarena a Shadawanka, Bauchi (a da ana kiran ta da suna
Semful) daga shekarar 1973 zuwa 1979, daga bisani kuma na wuce zuwa makarantar sakandire ta GSS Gumau a shekarar
1980, a 1982 ne kuma na samu canjin makaranta zuwa ‘Comprehensibe Day Secondary School’ da ke Bauchi, maganar da ake yi dai; ban ma kai ga kammala karatun wannan sakandire ba, ka dai ji yadda aka yi a takaice.
Yaya aka samu kai a gyaran rediyo tare da fara tunanin hada gidan rediyon da kuma watsa shirye-shirye?
Eh to, gaskiya ni tun ina dan firamare na ke koyon aikin gyaran rediyo, akwai wani mutum mai suna Alhaji Tawakkaltu; yanzu haka yana can Kasar Ogomosho, a wajensa ne na koyi wannan aiki na gyaran rediyo. Ina yin wannan gyara ne yau da gobe, sai nake cewa, ni fa zan yi gidan rediyo, daga nan ne na hada abubuwan da zan hada har ta kai ga an fara jin muryata tare kuma jin sautin gidan rediyona da yanzu ake iya jin ta a gidan kowa.
Har ila yau, sai da ta kai idan na kawo rediyo kusa da ni a lokacin da nake yin gyara, misali ina gyara daya a lokaci guda kuma ina jin daya rediyon kamar BBC ko Amurka, idan ina murda dayar; sai na ji sautin dayar na shiga cikin dayar, daga nan sai na tambayi kaina cewa, mene ne ya sa sautin wannan ke shiga cikin waccan rediyon, kawai sai na yi kokarin fadada bincikena, domin kuwa kullum ina da burin yin gidan rediyo a rayuwata.
Kwatsam! Watarana sai Allah ya taimake ni, idan ban manta ba; ranar 25 ga Febrairun 1980, ina cikin gwada sa’ata; ina murda tashar rediyo bayan na zabi Firikwansi, ina murdawa sai na yi nasara na kama tashar da babu kowa a kan layi; sai kawai na dora nawa layin a kai, bayan na fara samu sai na dauki makirfon dina na hada, idan na ce Hello sai na ji hade-hadena ya amsa
da cewa, “AAaa” amma kuma ba zan ji sauran ba, har aka zo inda nake jin haa, amma ba zan ji sauran ba kwata-kwata. Ina dai ta ci gaba da tunanin ya za a yi na kirkiri gidan rediyona na kaina, na dauki tsawon lokaci ina ta wannan fama.
A karshe yaya aka yi ka samu nasarar kirkirar naka rediyon?
A cikin wannan yanayi ne, wata rana na zo hutun makaranta lokacin ina Gumau, sai na ji labarin cewa akwai wani wanda ya hada gidan rediyo a wani kauye da ake kira Fingel, nan da nan na tashi na kama hanya na nufi garin, domin ganin wannan mutumin, sannan abin da zai ba ka mamaki shi ne, da kafa na taka na je har wannan kauyen. Na je na hadu da shi na kuma ga gidan rediyon da ya kirkira; duk kuwa da cewa gaskiya ba zan iya tuna sunan mutumin ba.
Bayan na je an kunna min rediyon na kuma ga yadda ya hada, ni ma bayan na dawo sai na sha alwashin bude nawa gidan rediyon, inda na zo na dukufa. A wancan lokaci, akwai wani irin abin tsara lokaci (time table) da ake amfani da shi na rediyo da na samu. Nan da nan, na harhada komatsena na samu zarafin fid da wannan gida na rediyo, a karon farko; waka kadai na rika sakawa. Nan da nan kuwa, sai jama’a suka fara yin tururuwa suna zuwa suna tambaya ta cewa, shin wai wane gidan rediyo ne suke sanya kida, amma babu magana?
Bugu da kari, a daidai wannan lokacin ma ba a san cewa; gidan rediyon nawa ba ne, sannan ga shi dai ina sanya wakoki amma wallahi a lokacin ban san yaya zan yi na hada ya yi magana ba, duk dai da cewa; na fara samun nasara ana iya jin wakokin da nake sa wa. A lokacin wakoki ne irn na da kamar irin su; ONAYO-ONAYO da KASKARA-KODIN da sauran makamantansu. Sannan a 1980 ne na fara watsa wadannan wakoki a gidan wannan rediyo nawa.
Bayan nan ne, Allah ya taimake ni na samu wani teb-rikoda, na yi jone-jonena har na samu yadda zan yi magana a ji. Duk yayin da zan yi Magana sai na ce; jama’a kuna tare da Wunty Rediyo?
Akwai wani dan’uwan mahaifina da ya zo ya samu mahaifin nawa yake tambayar sa cewa, ka ji labarin Audu ya hada gidan rediyo? Haka nan kowa ya rika mamaki.
Daga nan kuma me ya faru?
Daga wannan lokaci kuma sai duk gari ya dauka ana jin gidan rediyona, sannan sai na fara fita da rediyo ina zagawa don na san ina ne ake ji na, ina ne kuma ba a ji na? Da fari dai gidan rediyon nawa, da ‘yan dabaru na hada shi domin a rika ji na; har daga karshe na zo na fara samun dabarar yadda za a iya ji na a ko’ina.
A wane mataki aka fara jin ka a wannan tasha taka?
Kamar yadda na fada maka, da farko sai na hada antenan rediyo da rediyo ake iya ji, haka zalika da fari ma a dakina kadai nake iya jin abin da nake watsawa, daga kuma har Allah ya ba ni basira na sake samun yadda zan yi a iya ji na a waje, domin cikin ikon Allah, na samu basirar yadda zan yin a fitar da antenar waje, sannu a hankali har ta kai jihohi takwas suna iya jin wannan tasha tawa a wancan lokaci.
Ana watsa shirshiryen gidan rediyo ne ta hanyar amfani da Firikwansi, Kilohaz, Mita ko wani abu makamancin haka, ya aka yi naka babu wannan, amma ana iya jin ka?
Ai wallahi mutane da dama idan suka zo suka ga yadda gidan rediyona yake mamaki suke yi, suna gani kamar wani abu ne mai kama da tsafi. Don haka, kai tsaye na kan ce da su ba tsafi ba ne, baiwa ce daga Allah wadda ya yi min; dukkan rediyon da na samu zan iya amafani da ita tare da sarrafa ta ta fara watsa shirye-shirye nan take. Haka nan, a cikin minti biyar kacal zan iya hada rediyo na dawo da ita ritansimita a fara jin ta a duk gari.
Duk gari fa ka ce kuma a cikin minti biyar?
Kwarai da gaske, yanzu a yadda muke da kai din nan, a kan wannan teburin; idan na baje na’urorina a cikin kankanin lokaci zan iya cilla tashata a ji ta, kai ni har ma rediyon da za a iya hadawa a sanya a aljihu ta yada shirye-shirye, na iya hadawa yanzu; ina nan da su a ajiye. Hatta a jikin wayar hanset, ina iya hada gidan rediyo, yanzu haka ma ina da wanda na hada a gidan rediyo daga rediyo.
To yanzu yaya kake yi kake hadawa?
Da farko ina neman kwamfunet na rediyo, irin su tiransisto da rizisto. Tiransisto wani abu ne, yana nan mai kafa uku, amfaninsa ko aikinsa a jikin rediyo yin amfurfeyin ne na abun da ka hada masa, akwai wajen sa abu; nan ne ake sanya masa, sannan yana da wajen amsar abubuwan da aka hada masa. Don haka, amfaninsa yana da yawan gaske.
Baya ga wadannan abubuwa akwai kuma wasu abubuwan da kake nema kafin rediyonka ta yi aiki?
Kwarai ma kuwa, akwai eriya, makirfon da kuma kebul; da zarar na hada wadannan rediyona za ta fara aiki. Sannan kuma, kowace irin eriya ina iya hada ta ta zama kamar antena.
Da wace irin antena kake amfani da har ake jin ka a dukkanin fadin Jihar Bauchi?
Irin wannan antena na nan a jikin Sakatariyar Karamar Hukumar Bauchi. Kafin wannan lokaci, ina watsa wannan shirye-shirye nawa ne a wuri wanda karamar hukuma ta ba ni, a nan nake samu ina yin dan hade-hadena, daga nan kawai sai wani attajirin mai kudi ya zo ya mallaki shago, sai ya hade shagon da aka ban a nasa, har yanzu kuma antenar da nake amfani da ta na nan a sama, ko yanzu na je na hada za ka ji ni a dukkanin fadin Jihar Bauchi da sauran jihohi sama da takwas.
Ya maganar Firikwansi?
Wannan kamar yadda ka sani, na zaba na kai wajen masu sahalewa, sun duba tare da ba ni izinin ci gaba da amfani da shi. A wancan lokaci, Kamfanin Naitel ne suke ba da izinin amfani da firikonsi, don haka sai na rubuta na ba su; a lokacin Alhaji Maina shi ne shugaba wajen.
Mene ne naka firikonsi din?
Firikonsi dina shi ne 14.00kilohaz midiyon web ban. Sunan rediyona kuma Wunty rediyo.
Yanzu idan aka ce ka je wajen wani taro ka hada rediyonka ana ji a duniya za ka iya?
Kwarai kuwa, sosai ma cikin kankanin lokaci; zan hada a ji ni a kowane waje idan na ga dama.
Me da me kake bukata kafin ka hada?
Abin da kawai nake bukata shi ne tiransisto, rizisto da kafasto da kuma irin su tiransifoma, da zarar na samu irin wadannan abubuwa; an gama Magana nan take zan hada maka gidan rediyo, baya ga abubuwan da na zayyano; abubuwan da zan nema kari ‘yan kadan ne.
Da wutar lantarki ko jannareto kake amfani?
Na kan hada gidan rediyo da batir, sannan ina amfani da wuta ko kuma sola idan ina so, dukkaninsu ina amfani da su.
Yanzu kana aiki da gidan rediyon BRC, shin kana da burin inganta gidan rediyon, musamman ta fuskar na’urori?
Tabbas ina da burin hakan, amma gaskiya gidan rediyon Bauchi na bukatar sabbin kayan aiki na zamani, duk da cewa muna da burin kai gidan rediyon ga babban matsayi nan gaba in sha Allahu.
Wadannan abubuwan da ka bayyana, ana iya cewa baiwa ce ko kuwa a naka ganin iyawa ce?
Duka biyun ne, akwai baiwar akwai kuma iyawar. Domin tun ina dan aji hudu a firamare na ke koyon gyaran rediyo, sannan na kuma koya wa wasu da yawa.
Daga cikin wadanda ka koya wa akwai wanda ya iya hada rediyo kamar yadda kake hadawa?
A’a gaskiya babu, dukkaninsu babu wanda ya iya hada rediyo, amma dai sun iya gyara sosai.
Yanzu idan ina so ka koya min yadda ake hada gidan rediyo, zai yiwu ka koya min?
Me zai hana na koya maka idan da gaske ke? Misali, yanzu idan ka nemi rediyonka guda biyu, sai ka fara neman layin da babu kowa a kan firikonsi, bayan ka zaba za ka ji wani abu ya yi maka ausaloshin za ka ji ya zaba, kamar tasha ta bude; amma ba ta fara magana ba, a wannan lokaci ne za ka nemi hanyoyin da za ka hada tab dinka yadda kowa zai iya jin ka.
Ka ce ana jin ka a kusan jihohi takwas, wadane jihohi ne?
Tabbas idan ana iya ji na a Jihohin Kano, Adamawa, Gombe, Taraba, Jos kai har ma da Kasar Nijar. Sannan kuma wallahi, idan na hada ka zo ka ga wajen da kuma na’urorin, idan aka ce da kai a wannan tashar ake jin kaza; sai ka musanta. Da yawan ‘yan jarida sun yi aiki a gidan rediyona, sun iya ta hanyar wakoki da gaishe-gaishe da kuma wasan kwaikwayo, duk
na sha yi.
Ka ce kana da antena a sakatariya mene ne ya kai ka wajen?
Kamar yadda na fada maka a baya cewa, a da ina da shago a wajen, ina kuma hada shirye-shiryena; amma yanzu an karbe shagon a wajena, duk da haka kuma ina so bayan na yi ritaya na kammala aikin gwamnati, zan hada gidan rediyona na ci gaba da watsa shirye-shiryena.
Mene ne burinka a rayuwa?
Babban burina shi ne na ga na koyar da wasu daga cikin al’ummar kasar nan gyara da kuma fasahar zamani. In na kammala aikina, zan bude gidan rediyo nawa na kaina. Yanzu haka, ina da burin ganin gidan rediyon da ke hannuna na inganta shi, sannan bayan na kammala aikin zan nemi shago na ci gaba da watsa shirye-shiryena na kaina.
Da za ka samu wani tallafi daga gwamnati ko wasu kungiyoyi, shin za ka bunkasa wannan gidan rediyo naka?
Ko shakka babu, da zan samu wani tallafi ko gudunmawa da kuwa na hada tashar da babu irin ta a kaf wannan yanki namu,
ko Nijeriya ma sai ta yi dakyar za ta samu gidan rediyon da zai kai nawa. Domin na san abubuwa sosai a kan rediyo, wanda baiwa ce da Allah ya ba ni. Haka zalika, ina da wata na’ura da na hada; kawai da ita nake yin jone-jonena, sai kawai ka ji ana jin muryata.
Bayan gidan rediyon Bauchi BRC, ka taba zuwa wani waje ka yi aikin na’urori?
Akwai gidajen rediyon da yanzu haka ina daya daga cikin wadanda suka jera musu na’urori da yawa, sannan kuma na sha zuwa taruka da bita a kan na’urori da sauran makamantansu, domin bunkasa gami da kara samun ilimi kan harkokin na’ura.