Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a jiya Litinin ya gana da ministar harkokin wajen jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Sylvie Baipo-Temon a nan birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin inganta hadin gwiwa a fannoni daban daban.
Wang Yi ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana daukar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a matsayin aminiya kuma abokiyar hulda. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wajen gano hanyoyin samun bunkasuwa da ta dace da yanayin kasarta, da kuma yin magana da yawun kasar a kwamitin sulhu na MDD da kuma a bangarori daban daban.
A nata bangaren, Baipo-Temon ta nuna jin dadinta ga yadda kasar Sin take tsayawa tsayin daka kan ka’idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe. Tana mai cewa, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na mutunta ka’idar Sin daya tak, kana tana goyon bayan kasar Sin sosai wajen kiyaye manyan muradunta. (Mai Fassarawa : Yahaya Mohammed)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp