Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai a yau Talata, inda ya gayyaci mataimakin shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin Sheng Laiyun, don ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin Sin ya kasance a watan Janairu da Fabrairu da Maris na bana.
Bisa alkaluman da ya gabatar wa taron, yawan GDPn a wadannan lokuta ya wuce dala triliyan 4, wanda ya karu da kashi 5.3% bisa na makamancin lokacin bara, wanda kuma ya karu da kashi 1.6% bisa na watannin Oktoba da Nuwamba da Disamban bara. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp