Rundunar jami’an tsaro da ta kunshi Sojoji, DSS, ‘yansanda, Civil Defence da kuma ‘yan banga, sun kubutar da wasu mata biyu daga hannun masu garkuwa da mutane.
An yi nasarar kubutar da matan biyu da harin ya rutsa da su ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro a kananan hukumomin Maiyama da Suru na jihar kebbi.
- Gwamnatin Katsina Ta Raba Wa Jami’an Tsaro Sabbin Motocin Yaki
- Da Ɗumi-ɗuminsa: Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Fara Binciken Gwamnatin el-Rufai
Darakta mai kula da harkokin tsaro, Abdulrahman Usman ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wani taron manema labarai a jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa, ‘A bisa umarnin da Gwamna Nasir Idris ya bayar ga rundunar hadin guiwa na bin diddigin masu garkuwa da mutane bayan da labarin sace matan biyu ya iso gare shi, nan take jami’an tsaro suka fara daukar mataki.
Tawagar jami’an tsaron ta hadin kai, sun fatattaki ‘yan fashin daga dajin garin Giro zuwa Boma, har zuwa dajin Zugu Liba inda aka ceto matan biyu a cikin koshin lafiya’.
Daraktan ya ci gaba da bayanin cewa, a lokacin da masu garkuwan suka kasa iya jurewa matsin lamba daga jami’an tsaron, sai suka tsere suka bar matan da suka yi garkuwa da su.
A cewarsa, an samu nasarar mika matan biyu ga shugaban karamar hukumar Maiyama, Hon. Adamu Aliyu Liba kuma tuni aka hadu su da iyalansu.
Ya bayyana matukar godiya ga Gwamna Nasir Idris bisa irin gudunmuwar da ya ke bayar wa kan lamarin tsaro wanda ya kai ga samun nasarar ceto wannan matan biyu.