Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje da matarsa da dansa ba su halarci zaman babbar kotun jihar Kano ba a ranar Larabar nan domin amsa tuhumar da ake yi musu na cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudaden gwamnati.
In ba a manta ba, LEADERSHIP ta rahoto muku cewa, kotun ta sanya ranar Laraba 17 ga watan Afrilu, a matsayin ranar da Ganduje, da matarsa, Hafsat, da kuma dansa, Umar, za su gurfana a gabanta bisa zargin da gwamnatin kano ke musu na almundahana da kudaden al’umma.
- Kotu Ta Tabbatar Da Dakatar Da Ganduje Daga Shugabancin APC
- Ministan Harkokin Kasar Wajen Kasar Sin Da Takwaransa Na Iran Sun Tattauna Ta Wayar Tarho Kan Rikicin Isra’ila Da Iran
Lokacin da maganar ta zo gaban Mai Shari’a Usman Na’abba, lauyan Ganduje, Nureini Jimoh, ya ce, ba a gurfanar da wanda yake karewa ba, don ba a mika masa takardar gayyata ba hannu-da-hannu ba.
Amma lauyansa, Nureini Jimoh ya kasance a kotun yayin da sauran wadanda ake tuhuma duk ba su halarci kotun ba.
Lauyan gwamnatin jihar Kano, Y. A. Adamu, ya shaida wa kotun cewa, ba za su iya baiwa wadanda ake kara takardar gayyata hannu-da-hannu ba.