Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar ta yi matukar damuwa, tare da bayyana adawa da aniyar kasar Amurka ta kaddamar da bincike karkashin sashe na 301, mai kunshe da korafe-korafe don gane da hada-hadar sufurin jiragen ruwa ta Sin, da ta aikewa da hajoji da ta kera jiragen ruwa.
Cikin wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar a jiya Laraba, ta ce Amurka ta kitsa zarge-zarge marasa tushe, kuma korafe-korafen sun jirkita gaskiya, tare da kallon hada-hadar cinikayya da zuba jari da aka saba da su a matsayin harkoki masu barazana ga tsaron Amurka, da moriyar kamfanoninta. Kaza lika, Amurka ta dora alhakin matsalolin da masana’antunta ke ciki kan kasar Sin, duk da rashin wasu shaidu na hakika, da sabawa kyakkyawar fahimtar tattalin arziki da hakan ke nunawa.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ko shakka babu zarge-zargen na Amurka ba su da tushe ko makama, duba da cewa ci gaban masana’antun kasar Sin sakamako ne na kirkire-kirkiren fasaha, da yadda kamfanonin kasar ke shiga a dama da su cikin takarar kasuwanni. (Saminu Alhassan)