A halin yanzu an kammala shirye-shieyen bude bikin baje kolin motoci na yankin Afrika ta Yamma karo na 4 a ranar 14 zuwa 16 ga watan Mayu, na wannan shekarar a Landmark Centre, Bictoria Island, da ke Legas za a gudanar da shi.
Ana sa ran masu baje koli fiye da 250 za su shiga shirin ana kuma sa ran za a samu malarta taron fiye 4,500 da za su zo daga sassan duniya.
- Amurka Na Fakewa Da Guzuma Domin Harbin Karsana
- Sharhi: Daidaiton Da Sin Da Jamus Suka Cimma Zai Taimakawa Kawar Da Ra’ayi Maras Kyau Daga Yammacin Duniya
Taron baje kolin zai gudana ne a karkashin jagorancin shugaban hukumar samar da motoci ta kasa, Lukman Mamudu. A jawabinsa, ya bayyana cewa, taron baje kolin zai samar wa da masu ruwa da tsaki a sashin damar tallata hajojinsu da kuma tattaunawa da gamnatocin yankin Arfika ta Yamma a kan yadda za su ci gajiyar juna a fannin samar da motoci masu saukin kudi da kuma motoci masu amfani da iska gas da kuma masu amfani da wutar lantarki musamman ganin ana yekuwar kauce wa amfani da man fetuur saboda yadda hayakin ke cutar da muhalli.
“Sanin dokoki da ka’idojin gudanar da taron baje kolin zai taimaka wa masu halartar taron fahimmtar yadda za su zuba jari a bangaren da za su samu ribar da ya kamata, musamman a wannan lokaciin da ake karfafa gudanar da kasuwanci a tsakanin kasashen yankin Afrika ta yamma da ma yankin Afrika gaba daya,” in ji shi.