A yau Laraba, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Anthony Blinken, ya fara ziyarar aiki karo na biyu a nan kasar Sin a wa’adin aikinsa. Kafin fara ziyarar tasa, ‘yan siyasar Amurka sun yi ta yayata labarai ta kafofin yada labarai kan wasu batutuwa, da nufin kara masa karfi a bangaren shawarwarin da zai gudanar da Sin.
Bisa labarin da kafofin yada labarai na Amurka suka bayar, an ce, Blinken zai ci gaba da aikin Janet L. Yellen, na shafawa kasar Sin bakin fenti, kan wasu bangarorin da Sin take da fifiko bisa Amurka, da kalaman wai “Yawan kayayyakin da masana’antun Sin ke samarwa ya wuce kima”. Kafofin yada labaran Amurka su kan yayata irin wadannan labarai, a duk lokacin da Sin ke da fifikon karfin takara a masana’antun makamashi mai tsabta. Dalilin dai shi ne, ‘yan siyasar kasar na da matukar damuwa kan bunkasuwar sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko a kasar ta Sin.
- Sin Ta Yi Kira Ga G7 Da Ta Sauya Tsohuwar Halayyar Dora Alhaki Kan Wasu
- Jami’in Ma’aikatar Wajen Sin Ya Yi Tsokaci Game Da Ziyarar Sakataren Wajen Amurka A Kasar
Alal hakika, yawan motoci masu amfani da makamashi mai tsabta da Sin ta samar bai wuce kima ba. A maimakon haka, bai kai ma yawan da ake bukata a duniya ba. Ana bukatar karin irin wannan motoci, don tabbatar da hana fitar da hayaki mai dumama yanayi a duniya.
A matsayin kasa mafi karfi a fannin samarwa, da sayar da motoci masu amfani da makamashi mai tsabta, kasar Sin ta samar da motocin da yawansu ya kai fiye da miliyan 9.5 a bara, kuma ta fitar da kimanin miliyan 1.2 ketare. Adadin da ya kai kusan kashi 90% na biyan bukatun cikin gidan kasar ta Sin. Abin da ya alamanta cewa, duniya na matukar bukatar motocin da Sin ke kerawa, kuma karfin Sin na samar da motocin na da babbar ma’ana ga duniya, wanda sauran kasashe suka gaza samarwa.
Burin ‘yan siyasar Amurka shi ne mai da fari ya zama baki, bisa fifikon da Sin take da shi, har su mayar da hakan barazana, don hana bunkasuwar Sin a wannan bangare, kuma matakin da suke dauka tamkar munafunci ne. (Amina Xu)