Fursunoni 119 sun tsere daga gidan yari a karamar hukumar Suleja a jihar Neja sakamakon wani ruwan sama da ya ruguza katangar ginin a daren Laraba.
Ruwan saman da ya dauki tsawon sa’o’i yana zuba a daren ranar Laraba, ya lalata wani bangare na gidan yarin da suka hada da katangar da ke kewaye da gidan, lamarin da ya ba wa fursunonin damar tserewa cikin sauki daga gidan.
- An Gudanar Da Bikin Murnar Ranar Harshen Sinancin MDD Na Shekarar 2024
- Amurka Ta Jirkita Gaskiya Game Da Kayayyakin Dake Amfani Da Sabbin Makamashi Na Sin
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na gidan, AS Duza, ya fitar, ta ce, hukumar nan take ta fara gudanar da ayyukanta na kamo wadanda suka tsere, tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, an cafko fursunonin guda 10 da suka tsere yayin da ake kan gaba wurin cafko sauran.
Ya kuma roki jama’a da su kai rahoto ga ofishin jami’an tsaro mafi kusa ga duk wani fursuna da suka gani yana tserewa.