• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Saudiyya Ta Ba Nijeriya Kyautar Tan 50 Na Dabino

by Yusuf Shuaibu
1 year ago
in Labarai
0
Saudiyya Ta Ba Nijeriya Kyautar Tan 50 Na Dabino
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar Jumma’ar nan ne gwamnatin Saudiyya ta bai wa Nijeriya kyautar dabino tan 50 a yunkurinta na inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Faisal Ebraheem Alghamdi, ne ya mika dabinon yayin wani biki da aka gudanar a Abuja.

  • Gini Ya Danne Magina 15 A Jihar Kano
  • An Kaddamar Da Bikin Nune-nunen Shirye-shiryen Bidiyo Da Sinima Na Kasar Sin A Kasar Serbia

A cewarsa dabinon kyauta ce daga Sarkin kasar, kuma Babban Hadimin Masallatan Harami guda biyu, salman Al-Saud. Ya ce gwamnatin kasar, ta hannun Hukumar Bayar da Agaji ga Kasashen Waje ta Kasar (KSRelief), ta jima tana bayar da tallafi ga gwamnatin Nijeriya ta fuskoki da dama.

Ya ce daga cikin irin shirye-shiryen, akwai tsarin tallafi na Et’am, wanda ya tallafa a watan Maris shekara ta 2024 da abinci ga mutum 5606 a jihohin Kano da Jigawa da Katsina da Borno da kuma Abuja, wanda ya lashe Dalar Amurka 400,000.

Haka kuma a cikin sanarwar da ta fito daga ofishin jakadancin kasar a Najeriya ya ce Cibiyar Jin kai ta Saudiyya na shirin yin gangamin bayar da tallafin lafiya a Abuja da kano da kuma Legas, kuma za a yi ne a watanni uku karshen cikin shekara ta 2023.

Labarai Masu Nasaba

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

Da yake karbar wannan kyautar dabinon, mataimakin darakta mai kula da yankin kasashen gabas ta tsakiya a ma’aikatan kula da kasashen waje, Ambasada Murtala Jimoh ya nuna godiyarsu ga gwamnatn Saudiyya inda ya ce Najeriya da ‘yan Nijeriya suna godiya da wannan gagarumin aikin na jin kai.

Ya kara da cewa dabinon za a mika wa ma’aikatan jin kai

“A cikin ma’aikatan ne, za mu tabbatr da cewa duk wadanda suka cancanta sun samu wanda za su kasance mabukata ne da suke bukatar dabinon,” kamar yadda ya fada.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: DabinoKyautaNijeriyaSaudiyya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gini Ya Danne Magina 15 A Jihar Kano

Next Post

Yanzu-yanzu: Wasu Magina Sun Makale A Baraguzan Wani Gini Da Ya Rushe A Kano

Related

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya
Manyan Labarai

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

1 hour ago
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC
Labarai

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

4 hours ago
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi
Labarai

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

5 hours ago
Daurarru
Labarai

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

14 hours ago
Wutar lantarki
Labarai

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

16 hours ago
Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka
Labarai

Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

17 hours ago
Next Post
Yanzu-yanzu: Wasu Magina Sun Makale A Baraguzan Wani Gini Da Ya Rushe A Kano

Yanzu-yanzu: Wasu Magina Sun Makale A Baraguzan Wani Gini Da Ya Rushe A Kano

LABARAI MASU NASABA

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

June 7, 2025
Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

June 7, 2025
Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

June 7, 2025
Neja

Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja

June 7, 2025
Adawa

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

June 7, 2025
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

June 7, 2025
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

June 7, 2025
Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

June 6, 2025
Daurarru

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

June 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.