Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda game da batun matakin Amurka na zartaswa, da kuma sa hannu kan jerin kudurorin ba da tallafin soja ga kasashen waje, ciki har da masu nasaba da abubuwa marasa kyau dake shafar kasar Sin, Lin Jian ya ce kudurorin sun lahanta ikon mallakar yankunan kasar Sin, yayin da shirin ba da tallafin harkokin soja ga yankin Taiwan ya kasance matakin keta manufar kasar Sin daya tak, da kuma kudurorin dake kunshe cikin takardu uku da Sin da Amurka suka amincewa. Don haka bangaren Sin na matukar adawa da hakan, kuma ya riga ya shirya tattaunawa da bangaren Amurka game da batun.
Game da rahoto, mai taken “Barazana da lalacewa da Amurka ta kawo wa tsaro da ci gaban yanayin yanar gizo na kasa da kasa”, da kungiyar masu sana’ar tsaron yanar gizo ta Sin ta fitar, Lin Jian ya ce, bangaren Sin ya bukaci bangaren Amurka da ya yi biyayya ga ka’idojin kasa da kasa, ya kuma daina gurgunta zaman lafiya da kwanciyar hankali, da tsaron yanayin yanar gizo.
Game da hargitsi tsakanin Falasdinu da Isra’ila kuwa, Lin Jian ya ce, Sin ta dade tana goyon bayan bangarorin Falasdinu, wajen warware rikicin da suke ciki ta hanyar tattaunawa, kuma za ta ci gaba da kokarin yin hakan. Miliyoyin fararen hula dake zirin Gaza, suna bakin mutuwa, abun da ya dace shi ne a gaggauta tsagaita bude wuta. (Safiyah Ma)