Ci gaba daga makon jiya…
Na Biyar: Yana daga abin da Allah ya kirga wa Manzon Allah (SAW) na daga ni’imominsa ya tabbatar masa da shi a wajensa, cewa Allah ya shiryar da Manzon Allah (SAW) ya zuwa abin da ya shirya masa, ya shirya masa Shari’a; Annabawa dukkansu a kan tauhidi suke bare shi (SAW) a kan tauhidin Babansa Annabi Ibrahim (AS) yake. Dukkan Kuraishawa haka suke cikin tauhidin Annabi Ibrahim suke kafin zuwan Alkurani, bayan Manzon Allah ya yi Shekara 40. Ko kuwa ana nufin shiryar da mutane ga Manzon Allah (SAW) ko kuwa batacce ya same ka sai ya shirya ka (Ka san Alkurani Fasaha yake da shi don shi ake yin Tafsiri, don wani wajen sai an kara fassarawa ba wai yadda ka gan shi za ka dauke shi ba). Allah Ya same shi ba mawadaci ba, ba gidan kudi yake ba, amma ya fito gidan Imani sai Allah Ya wadata shi da abin da ya bashi, Allah ya wadata shi da kudin Sayyada Khadija, bayan haka da kudin Sayyadina Abubakar, bayan duk wadannan kudin sun kare, sai Ya wadata shi da kudin Ganima.
An yi ta yin yaki ana cin galaba ana samun ganima, sannan kuma da kudin Farhi, Mutane su zo su ba da gari da kansu ba tare da an fada su da yaki ba, to wannan kudin duk nasa ne (SAW) da Iyalansa da talakawa. Ko kuwa Allah ya wadata shi a cikin Zuciyarsa na daga yakana, don Manzon Allah (SAW) ya wadata da kadan, Har yake wa kansa Addu’a (Don yanzu in an ce mutum ya yi wa kansa wanna addu’a ba zai iya ba), “Allah ka sanya abincin gidana na yanzu ne na anjima sai an nema”: Sayyada Aisha ta ce sai ana yin kwana uku ba a dora tukunya ba, aka ce to me ye abincinki sai ta ce bakake biyu mana, meye bakake biyu? Ta ce Ruwa da Dabino sai dai akwai Makwabta sukan kawo wa Manzon Allah (SAW) Madara kyauta. Allah ya ba shi zabi ya zamo Annabi irin Sulaimanu, amma ya zabi ya zama idan yau an samu ya gode wa Allah, gobe ya rasa ya yi hakuri. Ya ce wannan daga Allah ne, ko kuma abin da Allah ya wadata shi da shi; shi ne Yalwar Zuci. An ce ita ce babbar wadata na daga yakana da ginar Zuciyarsa.
Allah ya same shi maraya sai Ya taro shi zuwa ga Baffansa ko kuma ya taro Baffansa zuwa gare shi, wato Abi Dalibi kuma ya sanya ma Abi Dalibi soyayyarsa wanda ko babansa ya tarar da rai iyakacin abin da zai masa kenan irin abin da Abu Dalibi ya yi masa. Manzon Allah (SAW) yana wata biyu a cikin Mahaifiyarsa babansa ya rasu, bayan an haife shi kakansa Abdul Muddalibi shi ya dauke shi, yana dan shekara biyu Abdul Muddalibi ya rasu tun daga nan ya zamo mahaifiyarsa ita ta dauke shi da Baffansa su suke kula da shi bayan ya kai shekara shida mahaifiyarsa ta rasu ya zama ba shi da kowa daga Allah sai Baffansa, toh baffan nan nasa da ya dinga kula da shi, ya so shi, ya kare masa har fiye da shekara hamsin da wani abu, shi ne Abu Dalibi.
Kila kuma Allah ya taro shi zuwa gare Shi (SWT), Haka Allah ya dinga kare shi duk daular Jahiliyya Allah ya kiyaye shi bai afka ko daya a ciki ba, an ce maraya kuma ya shiryu, to wannan abun mamaki ne. Kila Allah ya same shi maraya (Larabawa suna shiga cikin teku su debo kwansan gwal, wani a samu biyu, wani uku wani kuma a samu daya to sai su ce sun samu marayan gwal, wanda bai da abokin tarawa don ya fi tsada), toh ma’ana maraya shi kadai wanda bai da abokin tarawa. Allah ya taro ka ya b aka Annabta, ai ba wani gare ka. Kila ma’ana bai same ka ba ya shiryar da batacce da kai, ya wadatar da talakawa da kai, ya taro maraya da kai. Manzon Allah ya reni marayan Khadija, ta Aure shi kuma tana da marayan mijinta Hindu, toh kila wannan ake fada. Allah ya tanadar ma shi da wadannan darajoji, Allah bai bar manzon Allah (SAW) tun a kuruciyarsa ba. Tarihin kuruciyar Manzon Allah (SAW) duk a haddace yake tun kafin ya zo. Yahudawa ma su suka fi haddacewa don sun san shi kamar yadda suka san ‘ya’yansu, sannan mu kuma duk an ruwaito daga wajen kakanninsa sun fada, Malamai sun fada, Abbas ma ya fada cewa tun yana yaro maraya ne shi, don ya yi kiwon tumaki ma shi da bakinsa ya fada. Allah bai bar shi ba, kuma tun da Allah bai bar shi ba, ta yaya kuma bayan girma ya zo masa, shiriya ta zo sannan Allah zai bar shi?
Abu na shida: Kila kuma waccar ayar ta maraya a zahirance ake nufi don akwai sanda Halimatus Sa’adiyya ta kawo shi sai ta ajiye shi kafin ta juyo ba ta gan shi ba, tana ta neman sa har ta fada wa Abu Dalibi cewa ta zo da yaro Makka amma ba ta ga inda ya yi ba, suka bazama cikin Makka ana ta neman sa har Abu Dalibi ya kama labulayen Ka’aba yana rokon Allah ya nuna masa wannan jika nasa, Ikon Allah Abu Jahil ya dawo daga tafiya sai ya gan shi ya ce da shi yaro me ye sunanka sai ya ce Muhammadu, daga ina kake sai Manzon Allah (SAW) ya gaya masa, sai ya ce kila jikan Abu Dalibi ne, sai Abu Jahil ya dauko shi ya dora shi a bayan rakuminsa ya yi, ya yi rakumi ya tashi ya ki, sai rakumin ya ce da Abu Jahil ya za ka dora shugaba a baya sannan ka ce in tashi, toh sai ya dawo da Manzon Allah gaba sannan rakumi ya tashi suka tafi, shi ya zo ya fadi wannan abun da bakinsa, amma hakan ba ta sa ya yi Imani ba, a cikin Littafin Dala’ilin Nubuwwa an kawo wannan. Kila makiyinka ne ma ya kawo ka gida wanda zai zama babban makiyinka a karshe.
Kila kuma Marayar Khadija ake nufi, Manzon Allah ya karantar da mu yadda za mu rike maraya kar ka cutar da shi, kar ka wahalar da shi, ma’ana yadda za ka daki danka don ka shiryar da shi ko ka tarbiyyantar da shi to shi ma ka yi mai hakan, mai bara ma kar ka kore shi kar ka hantare shi, Allah ya kiyaye Manzon Allah (SAW) ma ya fi karfin haka, toh shi ne Sayyidina Usman ya sayo Dabino ya ce wannan nonon Dabinon Manzon Allah (SAW) ya kamata ya ci sai ya kawo masa to ashe Almajiri ya ga wannan Dabinon, sai da Sayyidina Usman ya fita Almajri ya zo ya yi bara Manzon Allah ya sa aka dauki wannan Dabinon aka ba shi, Sayyidina Usman ya tare wannan Almajiri ya ce don Allah Annabi (SAW) nake so ya ci ka yi min kudi in biya, Almajiri ya yi wa Sayyidina Usman kudi ya biya sai ya maida wa Annabi (SAW) wannan Dabinon. Almajiri ya kuma dawowa ya yi bara Manzon Allah (SAW) ya kuma ba shi, Sayyidina Usman ya kuma tare shi ya saya har sai da aka yi haka sau uku sai Almajiri ya kuma dawowa ya yi bara na hudu sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “yau wai maibara ne ya zo mana koko dan kasuwa”, aka ce a’a, ya ce “a bashi ko a gaya mai magana mai dadi”, wannan kuma sanar da al’umma ne gabaki daya.
Manzon Allah ya kasance mai bai wa mai nema ko da bai da shi, an ce wani lokaci wani Sahabi ya yi rokon Manzon Allah ya ce masa ka je ka ranta sai ka dora a kaina in na samu zan biya sai Abubakar ya ce “Ya rasulullahi Allah bai dora maka ba, ya ya za ka dora wa kanka?”, sai Fuskarsa ta baci sai da Bilal ya ce masa “Ka ciyar ya Ma’aikin Allah kar ka ji tsoron talauci”, sannan Fuskarsa ta yi Murmushi. Toh haka ana magana da shi amma kuma da mu al’ummarsa ake yi.
Abu na bakwai: Allah ya hori Manzon allah (SAW) da ya bayyana ni’imar da Allah ya yi masa da gode wa abin da Allah ya daukaka shi da shi, don shi da yawa za ka ga Manzon Allah (SAW) yana bayyana ni’imomin da Allah ya yi masa a wasu Hadisai saboda godiya ne yake yi masa, haka ana son mutum idan Allah ya ba ka mulki ko kudi ko wani daukaka, toh ka nuna a ga abin a jikinka ba wai don alfahari ba da girman kai, a’a saboda godiya, ka nuna har a kyautar ka ma a gane, toh haka ya hore shi da shi da daukaka Ambaton Allah (Zikiri) amma ka yi magana da ni’imar Ubangijinka ka yi zance. Yana daga gode wa ni’ima, a rika fadar ta, wannan magana kebance ne ga Manzon Allah kuma ga al’ummarsa, ta game kowa da kowa. Alhamdu lillahi.