Hedikwatar tsaron Nijeriya, ta ce, sojojin da aka tura yaki da ‘yan ta’adda a fadin kasar nan sun kashe ‘yan ta’adda 715 sun cafke wasu 146 tare da kubutar da mutane 465 da aka yi garkuwa da su a watan Afrilu.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani karin haske kan ayyukan soji.
- Darajar Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashe Mambobin BRICS Ta Karu Da Kaso 11.3 A Rubu’in Farkon Bana
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutane A Katsina Da Filato
Janar Buba ya ce, sojojin sun kwato makamai iri-iri 937, alburusai iri-iri 23,034 da kayayyakin sata da darajar su ta haura Biliyan N2,572,397,190.00 a tsawon wannan lokacin.
Daraktan ya kuma jaddada cewa, kudurin da sojojin ke da shi na fatattakar kungiyoyin ‘yan ta’adda ba abu ne da za a tattauna ko a yi sulhu ba a kansu.
Janar Buba ya kara da cewa, a cikin watan sojojin sun gudanar da hare-hare da suka hada da kwanton bauna, kai samame, sintiri na yaki da sauran ayyukan sirri.
Cikin nasara, dukka hare-haren da sojojin suka kaddamar, sun samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan.