• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Sin Da Faransa Game Da Yanayin Yankin Gabas Ta Tsakiya

by CGTN Hausa
1 year ago
Sin

Tsakanin ranakun 5 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki kasar Faransa bisa gayyatar da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi masa. A yayin ziyararsa a kasar, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan yanayin yankin Gabas ta Tsakiya.

A matsayin zaunannun mambobin kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin da kasar Faransa, sun hada kai wajen warware matsaloli, da fuskantar kalubalolin tsaro bisa dokokin kasa da kasa. Kaza lika kasashen biyu sun yi Allah wadai da dukkanin aikace-aikacen keta hakkin bil Adama, da kuma hare-haren da ake kaiwa fararen hula. Har ila yau, sun nuna adawa da aniyar kasar Isra’ila na kai hari birnin Rafah, kasancewar hakan zai haddasa mummunar bazaranar jin kai a yankin, kana sun yi Allah wadai da matakin tilastawa Falasdinawa yin kaura.

  • Xi Ya Yi Tsokaci Kan Hargitsin Palastinu Da Isra’ila Da Rikicin Ukraine

A daya bangaren kuma, shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, kana sun yi kira da a dawo teburin shawarwari, domin aiwatar da “daftarin kafa kasashe biyu” yadda ya kamata. Shugabannin Sin da Faransa, sun kuma jaddada matsayarsu, game da warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya, da kare ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa kan bahar Maliya da gabar tekun Aden, da tabbatar da bin dokar tsagaita bude wuta a yayin gasar wasannin Olympics, da ajin gasar na nakasassu na lokacin zafi na shekarar nan ta 2024, wanda za a gudanar nan gaba a kasar ta Faransa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang).

LABARAI MASU NASABA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
Daga Birnin Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Next Post
Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki 

Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki 

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.