Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba za a fara jigilar kayayyaki a sabon layin dogo daga Legas zuwa Kano a watan Yuni, 2024.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin kwangilar da ke kula da aikin – kamfanin China, CCECC, ya sanar da cewa, tuni ya hada layin dogon har zuwa tashar sauka da dibar kaya ta Zawaciki da ke Dala a cikin birnin Kano.
- Lokaci Ya Yi Da Za A Kara Dakon Zumunci A Tsakanin Sin Da Serbia
- Sin: Haramta Fitar Da Kwakwalwar Kwamfuta Ga Huawei Da Amurka Ta Yi “Barazana Ce Ga Kasuwanci”
CCECC ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a lokacin da Ministan Sufuri, Sanata Sa’id Alkali, ya ziyarci wurin domin duba aikin a jihar Kano.
Ministan ya ce, fara ayyukan dakon kaya zai kara karkon manyan titunan kasar nan tare da ceto matafiya da ke mutuwa sakamakon hatsarin mota.