Da maraicen ranar 9 ga watan Mayu, agogon wurin, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, madam Peng Liyuan, da uwargidan firaministan kasar Hungary, Aniko Levai, sun ziyarci makarantar koyar da harsunan Sinanci da Hungary dake birnin Budapest.
Madam Peng ta ce, makarantar, kyakkyawar alama ce dake shaida zumuncin kasashen Sin da Hungary, kuma tana matukar farin-cikin ganin yadda daliban makarantar ke jin harshen Sinanci sosai. Tana kuma fatan ganin daliban za su kara kokari wajen koyon harshen Sinanci gami da al’adun kasar Sin, da ziyarta ko kuma yin karatu a kasar, domin bayar da gudummawarsu ga kara sada zumunta tsakanin kasashen biyu.
An kafa makarantar koyar da harsunan Sin da Hungary mallakar gwamnatin Hungary a shekara ta 2004, inda ake amfani da harsunan biyu don koyar da dalibai. (Murtala Zhang)