A yau Laraba ne kotun daukaka kara da ke garin Akure a jihar Ondo ta tabbatar dan takarar gwamna a jihar Osun a jam’iyyar PDP a jihar, Ademola Adeleke wanda ya lashe zaben na gwamnan jihar da aka gudanar a satin da ya wuce.
Kotun ta kuma yi watsi da karar mai neman takara, Dotun Babayemi, ya shigar a gabanta kan kalubalantar Adeleke a matsayin dan takarar gwamnan na PDP.
- Ba Mu Taba Tunanin Za Mu Fadi Zaben Osun Ba- Adamu
- Yawan Tashar Sadarwa Ta 5G Da Sin Ta Gina Ya Kai Kusan Miliyan 2
Babayemi dai ya shigar da karar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke a garin Osogbo, inda ya bukaci kotun ta ayyana shi a matsayin dan takarar gwanma na PDP a jihar.
In ba a manta ba, a ranar 8 Maris ne bangarori biyu a jam’iyyar PDP suka gudanar da zaben fidda-gwani a tsakanin takarar Adeleke da Babayemi amma kwamitin zartarwa na PDP na kasa ya goyi bayan Adeleke.
Har ila yau, a cikin sunayen Da INEC ta fitar ya nuna sunan Adeleke a matsayin dan takarar na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben fidda-gwanin.
Biyo bayan yanke hukuncin da kotun ta tarayyar ta yi ne, hakan ya sa Babayemi ya garzaya zuwa kotun daukaka kara, inda a nan ma ya yi rashin nasara.