Shugabannin mata na jam’iyyar APC a dukkan jihohi 36 na kasar nan ciki har da Abuja sun bukaci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi amfani da ofishinsa wajen kara wa mata yawan guraben wakilci a jam’iyyar.
Shugabannin mata na jam’iyyar APC sun bayyana hakan ne a wata ganawa tare da mambobin kwamitin gudanarwa a Abuja, sun koko kan rashin samun kwarin gwiwa a majalisar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kuma na shugaban mata na kasa na jam’iyyar APC, Dakta Mary Alile.
- Da Dumi-Dumi: APC Ta Kori Dan Majalisar Wakilai, Aminu Sani Jaji A Zamfara
- Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa
Shugabar kungiyar mata na APC a jihohi 36, Misis Patricia Yakubu, ta tuno da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar Shugaban Tinubu a zabukan da ya gabata, ta yi zargin rashin alaka tsakanin ministocin da kungiyarsu, wanda ta bayyana cewa shi ne mafi kusancin jam’iyyar a matakin farko.
Ta ce, “Matan jam’iyyar APC suna jin zafin yadda aka yi watsi da su a cikin wannan gwamnati.
“Haka kuma muna jawo hankalin shugabanmu kuma babanmu cewa ya kamata a kirkiro shirin gwamnatin tarayya da zai kara wa mata wakilci a dukkan fadin kasar nan.
“Muna kira a gareka ka yi amfani da ofishinka wajen tattaunawa da ministoci da shugabannin ma’aikatu ta yadda za a saka mata a cikin shirye-shiryanmusu wanda zai kara musu kwarin gwiwa na goyon bayan jam’iyyar, musamman a jihohi,” in ji ta.
Haka kuma Misis Yakubu ta zargi shugabar mata ta kasa na jam’iyyar APC da rashin mika bukatocin kungiyarsu ta matan APC.