A kwanakin baya, tsohon firaministan kasar Faransa Jean-Pierre Raffarin, ya bayyana a yayin da yake zantawa da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, kasar Sin ta riga ta taka mihimmiyar rawa a duniya, kuma duniya na hasashen kyakkyawar makoma ga kasar Sin a fannoni da dama.
Raffarin ya bayyana cewa, da farko dai, ya kamata a nemi samun zaman lafiya, domin zaman lafiya shi ne gaban komai. Kasar Sin na da matsayi mai muhimmanci a kwamitin sulhun MDD, har ma da ragowar sassan duniya baki daya.
- Sin Na Maraba Da Kamfanonin Kasa Da Kasa Da Su Zuba Jari Da Aiwatar Da Hada-hada A Kasar
- Shugabannin Kasashen Sin Da Rasha Sun Gudanar Da Wani Karamin Rukunin Tattaunawa
Ya ce, kasar Sin na sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a duniya, kana jama’ar kasar Sin ba su taba tada yaki a kasashen waje ba, don haka ake fatan kasar Sin za ta iya tsayawa tsayin daka kan ra’ayinta na kiyaye zaman lafiya.
Na biyu, ana nuna kyakkyawan fata ga makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya zama daya daga cikin manyan karfi dake ingiza samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya, yayin da sassan kasa da kasa ke mai da hankali ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin, musamman bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a kasar Sin, kasancewarsu karfin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin.
Na uku, ana nuna kyakkyawar makoma ga jama’ar kasar Sin wajen kirkire-kirkire. Matasan kasar Sin suna da basira da kwazon aiki, da kuma bunkasa kirkire-kirkire. Duniya tana bukatar kirkire-kirkire, kuma kasar Sin babbar kasa ce a fannin kirkire-kirkire. (Zainab Zhang)