Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta sallami daya daga cikin jami’anta daga aiki tare da rage wa wasu jami’anta uku matsayi kan zarginsu da hannu a wasu ayyuka na rashin da’a da aikata laifuka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce matakin ya biyo bayan cikakken bincike da aka yi wanda ya tabbatar da hannunsu a ayyukan rashin da’a da laifuka da dama.
- Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 386 Bayan Garkuwa Da Su Shekara 10 A Dajin Sambisa
- Zan Goyi Bayan Peter Obi A 2027 Matsawar PDP Ta Sahale Masa Yin Takara – Atiku
Ya ce an kori Sufeton ne bisa laifukan hadin guiwa da ɓata gari da fashi da makami dama garkuwa da mutane da almundahana.
A cewarsa, jami’in da aka kora tare da wasu mutane biyar ana zargin ‘yan kungiyar fashi da makami ne da suka yi wa wani mutum fashin kudi naira miliyan 29.8 a Gwagwalada da ke birnin tarayya Abuja, tare da ɗaukar nauyin garkuwa da wani mai suna, Ikechukwu Okafor, a Tunga Manje da ke Abuja, inda suka karbi Naira miliyan 4.4 a matsayin kudin fansa.
Kakakin ‘yansandan ya ce an gurfanar da jami’in da aka kora a kotu dan girbar abinda ya shuka, sauran jami’an uku da ke aiki da rundunar a bangaren ‘Special Tactical Squad’ (STS) an rage matsayinsu zuwa na baya wato Sajan, saboda tilastawa wasu mutane masu ababen hawa biyan kuɗi a Abuja.
“Al’amarin ya fallasa ne lokacin da wani Harrison Gwamnishu (@HarrisonBbi18) ya ba da rahoto, ta dandalin sada zumunta na zamani – ‘X’, inda rundunar ta yi bincike sosai kan lamarin.