Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta sanya karin wasu kamfanonin Amurka, a jerin kamfanonin da ba za a iya dogaro da su ba, bisa zargin su da hannu cikin hada hadar sayarwa yankin Taiwan makamai.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar a Litinin din nan, ta ce kamfanonin da aka sanya cikin jerin a wannan karo, sun hada da General Atomics Aeronautical Systems, da General Dynamics Land Systems, da Boeing Defense, da Space & Security. Sakamakon matakin, za a haramtawa kamfanonin gudanar da duk wasu harkokin shige da fice masu nasaba da kasar Sin, kana an haramta musu zuba sabon jari a kasar.
Kaza lika, an haramtawa manyan jami’an kamfanonin shiga kasar Sin, za kuma a kwace takardun su na aiki a kasar, kana za a soke shaidar su ta zama a kasar. Har ila yau, ba za a amince da duk wasu bukatu da suka gabatar ba. Sanarwar ta ce an dauki wadannan matakai ne domin kare ikon mulkin kai, da tsaro da ci gaban moriyar kasar Sin.(Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)