Ministocin harkokin wajen Nijeriya da jamhuriyar Benin, sun gudanar da shawarwarin kasashen biyu kan inganta tabarbarewar kasuwanci da cinikayya a tsakanin ‘yan kasashen biyu.
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Alhaji Yusuf Tuggar, ya ce, taron tuntubar junan, ya samo asali ne bisa umurnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Benin, shugaban Patrice Talon suka bayar na karfafa huldar zamantakewa da tattalin arziki tare da fadada kasuwanci tsakanin al’ummar kasashen biyu.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Aikin Ilimi Ya Shaida Kokarinsu Na Kafa Al’umma Mai Makomar Bai Daya
- Jirgin Sama Ya Yi Hatsari A Sama, Mutum 1 Ya Mutu 30 Sun Jikkata
Taron da aka yi a kan iyakar Segbana a jamhuriyar Benin, yana da nufin dawo da mashigar tsakanin iyakar Tsamiya a Nijeriya da kuma Anguwar Sule Wara a Jamhuriyar Benin zuwa rayuwa ta hanyar raya ababen more rayuwa da suka dace da sabon fatan da shugaba Tinubu ya ke dashi.
Tuggar ya bayyana cewa, an kara samun ci gaba wajen karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, don kara kasance ‘yan uwan juna a yammacin Afirka.
A nasa jawabin, Babban Kwanturola na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Bashir Adewale-Adeniyi, ya ce, taron an yi shi ne domin ciyar da yankin gaba tsakanin kasashen biyu da shugabannin kasashen biyu suka riga suka kirkiro.