Cigaba daga satin da ya gabata…
Na biyu kuma kina iya samun kwai kamar guda uku, ki fasa su, ki samu tumaturi manya guda uku, ki zuba dafaffen zogale a matsayin albasa, amma ya fi albasar da kike sakawa yawa. Ki sa Maggi, Gishiri yaddah ki ke so, ki juya, sosai sannan ki soya.
Suyar ba za ta kafe ba, za ta dagargaje, ta yi miki ruwa-ruwa, ki zauna ki cinye.
Idan kina da madarar shanu, ki dora a kai. Idan babu ki sami kamar Yoghurt ko nonon shanu, ki kara masa ruwa, ya yi tsululu, ki sa Suga ko zuma kadan, ki juya sannan ki shanye.
Irin wadannan abincin nau’in-nau’in suna da kyau mata su rika amfani da su a kowane lokaci. Haka ma Kwai, kamar yadda kowa ya sani ne cewa dafaffen kwai ya na daya daga cikin nau’o’in kayan abincin da ke gina jiki. Kazalika da yawa daga mutane ba su san cewa kwanduwar dake tsakiyar kwai ta fi farin da ke kewaye da ita fa’ida a bangaren gina jiki, kara lafiya, kuzari tare da sanya kwarin jiki ga dan Adam ba.
Da akwai labaran kanzon kurege da aka jima ana yayatawa, cewa wai duk wanda ke cin kwanduwar kwai akwai yiwuwar ya kamu da ciwon zuciya, wannan dalili ne ya kan sa wasu mutune ya cire kwanduwar kwan su jefar a sau da dama, sannan su cinye ragowar farin dake kewaye da ita.
Dangane da wannan jita-jitar ne ya sanya ni sha’awar tantancewa tare da fitar da gaskiya dake tattare da lamarin ta hanyoyin binciken da masana lafiya a duniya suka fitar.
Kamar yadda binciken ya nuna, cin dafaffen kwai tare da kwanduwarsa baki daya, yana matukar rage kiba tare da sanya koshin lafiya. Saboda haka, jefar da kunduwar kwai ba dabara ba ce, idan aka yi la’akari da irin rawar da take takawa wajen gina jiki da kuma kara ingantacciyar lafiya ga jikin bil-Adama.
Haka zalika, kai tsaye za a iya cewa, cin dafaffen kwai a matsayin karin kumallon safe ga dan’Adam, na yin tasiri ta yadda duk wani abu da aka ci wadda ke sanya kiba, to ko kadan a wannan ranar ba zai yi tasiri ba.
Har ila yau a wani binciken da aka gudanar a kasar Amurika, ya nuna cewa, wadanda ke amfani da dafaffen kwai a matsayi karin kumallon safe ba za su taba zama daya da wadanda ba sa yi da shi ba, ta fuskar rage kiba, tare da sanya kuzari da kuma yalwata lafiyar jiki baki daya.
A wani bangare kuma, idan mace na da bukatar rage kiba, to abu mafi sauki da ya kamata ta yi a takaice shi ne kamar haka:
Abu na farko da za ta nema shi ne zogale, bayan an gyara an wanke shi, sai a markada, sannan a tace ruwan, kana a rika sha safe da kuma dare, ma’ana kullum sau biyu a rana.
Sai dai kar a manta binciken ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sanya gudawa, saboda an hau turbar rage kiba ne.
Muddin aka yi amfani da wannan dabara kamar yadda aka bayyana, to mace za ta rage kiba sosai da sosai.
Sannan kuma ga wacce take da tumbi, sannan ta ke son rage shi, to sai ta sami sassaken Gamji ta hada da ‘yar jar kanwa, sannan a tafasa a rika sha, in Allah Ya yarda za a neme shi a rasa, saboda shi maiko yake tsotsewa a jikin dan Adam! Har ila yau shi zogalen ya na yin magunguna masu dinbin yawa.