Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON, Malam Jalal Ahmed Arabi ya mika ta’aziyya ga ‘yanuwa da iyalan Marigayya Hajiya Tawakaltu Busare daga Jihar Kebbi, ta rasu ne a garin Makkah.
Wakilin Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) a garin Makkah Dr Aliyu Tanko ya mika sakon a madaddin Shugaban.
- Alhazan Abuja Da Kogi Sun Yaba Wa Ƙoƙarin NAHCON A Madina
- Hajj 2024: NAHCON Ta Bukaci ‘Yan Jarida Su Yi Riko Da Gaskiya
A jawabinsa wajen ta’aziyyar, ya bayyana cewa, mutuwa na kan kowa a koyaushe kuma a ko ina. Daga nan ya umarci Ustaz Abubakar Lamin da ya yi addu’a ta musamman ga mamaciyar da fatan Allah Ya gafarta mata Ya Yi mata Rahama. Ya kuma sa muma mu cika da Imani idan tamu ta zo. Ta bangaren Hukumar jin dadin Alhazan Jihar Kebbi kuma. Alhaji Garba Takware, ya nuna jin dadin yadda kan ace kwabo har Shugaban NAHCON ya aiko wakilinsa da jami’ansa domin taya su alhinin wannan rashin. Ya ce a wannan abin a yaba ne.