Kungiyar gamayyar jam’iyyun adawa na ‘yan majalisar tarayya daga jam’iyyun siyasa daban-daban a karkashin kungiyar G-60 da suka hada da PDP, LP, NNPP da sauran su, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta bar sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da aka dawo da shi kan kujerar sarautar Kano cikin lumana.
G-60 ta jaddada cewa, bai kamata Gwamnatin Tarayya ta hargitsa Jihar Arewa maso Yamma ba, ta hanyar tsunduma cikin harkokin masarautun Kano, na cikin gida da ke karkashin ikon gwamnatin Jihar Kano.
G-60 da manyan ‘yan majalisar dokokin na goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano kan dawo da Sarki Sanusi II kan sarauta, wanda a cewarsu, tsige shi da kuma koranshi a baya, cin zarafi ne da wulakanta Sarauta.