Kwanan baya, yayin da shugaban kasar Kenya William Ruto ke ziyarar aiki a kasar Amurka, wani dan jarida na BBC ya taimbaye shi, ko yana kallon kasar Amurka a matsayin abokiyar hulda mafi samun karbuwa. Shugaba Ruto ya amsa da cewa, maimakon zabar bangaren yamma ko gabas, kasar Kenya ta fuskanci gaba. A ganina, wannan amsa ta nuna ra’ayin bai daya na kasashen Afirka, wato son samun ikon cin gashin kai don tabbatar da ci gaban kasa, maimakon daukar wani bangare saboda matsin lamba da aka yi musu.
Hakika a wannan zamanin da muke ciki, kasashen Afirka sun san salon raya kasa da kasashen yamma suka kakaba musu bai dace da yanayin da suke ciki ba, bayan yadda suka dade suna fama da matsaloli a fannonin tattalin arziki da tsaro. Saboda haka kasashen Afirka na kara nuna niyyar neman cikakken ikon cin gashin kai, da hanyar raya kasa da ta dace da yanayin da suke ciki. Wannan niyya ta sa shisshigin da wasu manyan kasashen dake yammacin duniya suka saba yi a nahiyar Afirka fara gamuwa da cikas. Wani misali a wannan fanni shi ne yadda jamhuriyar Nijar ta umarci sojojin kasar Amurka da su bar harabarta. Wani babban dalilin da ya sa Nijar daina hadin gwiwa da sojojin Amurka shi ne, yadda kasar Amurka ta nemi tsoma baki cikin harkokinta na diflomasiyya, lamarin da ya bata ran Nijar din.
- Ranar Yara Ta Duniya: Inganta Rayuwar Yaran Nijeriya Shi Ne Abu Mafi Girma – Tinubu
- Shugabancin JKS Ya Nazarci Matakan Gaggauta Raya Yankin Tsakiyar Kasar Da Kare Hadarin Harkokin Kudi
Kana a nashi bangare, shugaban kasar Congo Kinshasa Felix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, shi ma ya nuna rashin jin dadi kan yadda wasu kasashen yamma ke son ba da umarni ga kasashen Afirka, a lokacin da yake hira da wasu ’yan jaridan kasar Faransa. Inda shugaban ya ce, ya kamata kasashen yamma su sauya tunani, su kuma fara daukar kasashen Afirka a matsayin abokan hulda na gaske.
Ban da haka, a fannin kula da al’amuran kasa da kasa, kasashen Afirka su ma sun fara fito da murya daya, da kokarin ba da gudunmowa, don tabbatar da adalci a duniya. Misali, bayan da sabon zagayen rikicin Isra’ila da Falasdinu ya barke, kungiyar kasashen Afirka AU ta yi kira da a dakatar da yaki a zirin Gaza nan take, kana kasar Masar ta shiga tsakanin bangarorin dake yaki da juna ta hanyar gudanar da taron koli na neman sulhu na Alkahira, yayin da kasar Afirka ta Kudu ta kai kara gaban kotun kasa da kasa ta MDD, bisa zargin kasar Isra’ila da aikata kisan kare dangi don neman kawar da Falasdinawa daga doron kasa, inda kuma aka yanke hukunci bisa amincewa da karar da ta kai. Duk wadannan matakai, sun nuna yadda kasashen Afirka suke tsayawa kan kare ikon cin gashin kai, da kokarin kare adalci a al’amuran kasa da kasa, maimakon bin umarnin wani ba tare da tantance ainihin yanayin al’amura ba.
Sa’an nan, tarihi ya riga ya shaida amfanin kare ikon cin gashin kai a fannin raya tattalin arziki. Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta dade tana kasancewa cikin jayayyar da kasar Amurka da tarayyar Soviet ta USSR suka yi, bayan kafuwarta a shekarar 1949. Ta kuma taba fuskantar kalubaloli iri-iri, ciki har da yaki. Sai dai ta hanyar tsayawa kan ikon cin gashin kai da neman raya kasa karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kasar ta samu wata hanyar raya kai mai amfani, wato tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin. Bayan samun karuwar tattalin arziki mai dorewa cikin gomman shekaru, kasar Sin ta riga ta zama tattalin arziki mafi karfi na biyu a duniya, gami da kasar da ta fi karfin masana’antu, da cinikayya. Fasahohin kasar Sin a fannin raya tattalin arziki sun ba mu cikakken imani wajen yin kyakkyawan fata kan kokarin kasashen Afirka na raya kai: Matukar kasashen Afirka sun magance shisshigin da ake yi musu, da dakatar da yadda ake mai da su karkatacciyar kuka mai dadin hawa, to, tabbas za su samu tasowar tattalin arziki cikin sauri, bisa la’akari da dimin albarkatu, da matasa, da karfin kasuwanci da suke da su.
A sa’i daya kuma, ban da kasashen dake rungumar salon daukar matsaya 2, a ganin galibin kasashe wadanda suke tsayawa kan adalci, tabbatar da ikon cin gashin kai a cikin gida, na nufin nuna hakuri da kokarin hadin kai tare da sauran kasashe, inda za a yarda da ikon cin gashin kai na sauran kasashe. Saboda haka, a ganina, idan shugaba Ruto ya zo kasar Sin, to, ba za a taba yi masa tambaya cewa “ko kasar Sin abokiya ce da ta fi samun karbuwa” ba. Saboda ba kamar kasar Amurka, wadda take son raba kasashe zuwa rukunoni daban daban ba, a ganin kasar Sin dake da hakuri da son hadin gwiwa, kawai ana samun abokai ne, da wadanda za su zama abokai a nan gaba. (Bello Wang)