Shugaban kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA), Yakubu Maikyau, ya koka kan rawar da wasu lauyoyi da kotuna suka taka a kan hukunce-hukunce masu cin karo da juna dangane da rikicin masarautar Kano.
Wasu kotuna biyu a jihar Kano sun fitar da wasu umarnin wucin gadi masu cin karo da juna kan rikicin masarautar Kano.
- Majalisar Wakilai Za Ta Binciki CBN Kan Korar Ma’aikata 600
- Dattawan Kudancin Kano 103 Sun Buƙaci Gwamna Abba Ya Dawo Da Sarakuna 5 Da Aka Rushe
Mai shari’a S. A. Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Talata ya bayar da umarnin korar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II daga fadar Gidan Rumfa.
Sai dai mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da wani umarni na daban, inda ta haramtawa ‘yansanda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma rundunar sojojin Nijeriya daga korar Sanusi, ko muzgunawa ko kamawa.
Sarki Sanusi da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, na fafatawa da juna domin neman kujerar sarauta. Rikicin dai ya janyo zanga-zangar magoya bayan kowanne bangare a Kano.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Babban lauyan Nijeriya (SAN), Maikyau a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda lauyoyi da alkalan da ke da hannu a cikin shari’ar ke gudanar da ayyukansu.
Ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a sake yin nazari cikin gaggawa kan yadda kwararrun lauyoyi da alkalan da ke da ruwa da tsaki a wadannan al’amura ke gudanar da ayyukansu.
Shugaban NBA ya yi kira ga shugabannin kotunan da su binciki yadda alkalan ke gudanar da ayyukansu tare da kai rahoton bincikensu ga hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) domin daukar matakin da ya dace.