Ganin yadda akasarin Maniyyata da suka zo aikin Hajjin bana suna nuna karancin ilimin yadda ake gudanar da aikin hajji da kuma hukunce-hukunce ta, daya daga cikin Malamai da aka shigo da su daga gida Nijeriya domin fadakar da Alhazai a kasa mai tsari, Alhaji Malam Muhammadu, ya nuna takaicinsa a kan yadda jahiici ya dabaibaye mafi yawan alhazai arewacin Nijeriya, “yana matukar wahala ka iya koya wa wanda bai san wasu daga cikin ginshikan addini ba ya iya sanin yadda zai gudanar da aikin hajji karbabiya a cikin ‘yan kwanaki. A kan haka ya bukaci malamai su dage wajen shiya wa’azozi da tareukan fadakarwa ga al’umma don su samu ilimi na musamman a kan yadda za su gabatar da aikin hajji karbabe.
Tawagar Malamai a aikin hajji bana na karkashin shugabancin Malama Fatima Balori, cikin tawagar kuma akwai malaman addini maza da mata ciki har da Malama Rahinatu Ahmad, Maryam Aliyu da kuma shehin malamin nan na garin Abuja wato, Muhamamdu Nuru Khali wanda aka fi sani da “Digital Imam’, inda a nasa jawsabin ya jinjina wa irin shirye-shiryen da hukumar NAHCON ta yi musamman ta fannin gidajen da suka sauke maniyyata yankin Abuja, ya bukaci jami’an alhazai su kara kokari wajen gaggauta bayar da dakunan kwana, ya ce, yadda aka dade ana jiran a raba dakuna bai dace ba. Amma ya kuma koka a kan yadda wasu alhazai ke bata bayan daki, “Halayyar wasu alhazai yana iya zama babbar abin kunya ga kasa, a kan haka ya nemi a kara kaimi wajen fadakar da maniyyata a kan yadda za su tafiyar da harkokinsu.
Ya kuma bukaci maniyyata su kusanci malamai donmin sanin ka’idoji na gabatar da aikin hajji karbabbiya, “Yana da wahala a iya koya wa mutum yadda zai gudanar da aikin hajji a cikin dan karamin lokaci.