Nadin sarautar da Sarkin ‘Yandoton Daji ya yi wa jigo ga ‘yan bindiga da ya addabi jihohin Zamfara, Katsina da Sakwato, Ado Aleru ya tayar da kura, inda lamarin ya janyo dakatar da Sarkin ‘Yandoto Daji, Alhaji Aliyu Garba Marafa daga karagar mulki da kuma soke Sarautar Sarkin Fulanin da aka yi wa Aleru.
Wannan ne ya sanya LEADERSHIP Hausa ta garzaya yankin Masarautar Sarkin ‘Yandoto Daji domin jin ra’ayin al’ummar yankin na soke Sarautar Sarkin Fulani Aleru da shi kansa Sarkin ‘Yandoto da yanzu haka Gwamna Matawallen Maradu ya dakatar da shi.
Malam Alhassan Muntaka ‘Yankuzo, mazaunin ‘Yankuzo ne inda shi Sarkin Fulani Aleru yake da zama da iyalasa, ya bayyana wa wakilinmu cewa, Ado Aleru duk abubuwan da aka ce yana yi na ta’addanci bai taba yin su a Tsafe ta gabas ba.
Ya ce, “Duk fadin yankinmu na Tsafe ta gabas babu wani dan ta’addan da yake shigowa yankin domin cutar da mu. Kuma yanzu haka manomanmu da matafiyanmu suna gudanar da harkokinsu yadda ya kamata cikin ‘yanci tun kafin a ba shi sarautar Sarkin Fulani Tsafe ta Gabas.
“Zamowar Ado Aleru a yankin Tsafe ta gabas alheri ne a wajanmu, domin bai yarda a kawo mana hari daga baki da ‘yan gida ba. Kuma mutanansa masu kawo masa ziyara dauke da manyan makamai ba su taba cutar da mu ba. Domin haka soke sarautarsa ta Sarkin Fulani ba zai cutar da mu ba ko kadan,” in ji Muntaka ‘Yankuzo.
Hajiya Juma Banakowa, tana daya daga cikin mazauna Garin ‘Yankuzo kuma tana da gida a ‘Yandoto ta shaida wa wakilinmu ra’ayinta na soke Sarautar Sarkin Fulani Aleru kamar haka, Ado Aleru yana da gidaje a cikin ‘Yankuzo kuma yanzu haka nan yake da iyalansa.
Ta ce shi ba ya fita sai dai yana da yara dama, idan ka ga ba ya gari, to ya fita wajen Jihar Zamfara ko Kasar Nijer, domin can ya fi kai hare-harensa.
Juma ta kara da cewa, shi ne sila ta sulhu da aka yi a masarautar Tsafe wanda yanzu haka Fulani na shiga kasuwani, sannan matansu na sayar da nono.
A cewarta, yanzu a yankin Tsafe ta Gabas ba su da fargaba kuma warware rawanin Sarkin Fulani Aleru, ba zai fusata shi ba ya cutar da al’ummar yankin, domin dama bai saba cutar da su ba. Ta ce a yanzu haka yana neman auren wata budurwa a yankin kuma tana son sa duk da mahaifita ya ce ba zai ba shi ba saboda matansa hudu.
Batun dakatar da Sarkin ‘Yandoto kuwa, al’ummar garin murna ta koma cikin, saboda sabuwar masarauta ce wacce ba ta wuce wata biyu da kafa ta ba, kasancewar an cire ta ce daga cikin karamar hukumar Tsafe.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Mujitaba Damo, daya daga cikin mazauna ‘Yandoto, inda yanzu haka nan ne fadar masarautar Sarkin ‘Yandoto ya bayyana ra’ayinsu a kan wannan danbarwa kamar haka, “lallai ba a yi wa Sarkin ‘Yandoto, Aliyu Garba Marafa adalci ba, domin kafin sarkin ya rike wannan mukami ya taba zama uban kasa da hakimi bai taba yin abu ba tare da izini gwamnati ba, ballantana yanzu da ya zama ya samu matsayi na sarki mai daraja ta uku.”
Ya kuma kara da cewa ya san Ado Aleru babban dan ta’adda ne, domin haka sarkin bai da ikon ba shi sarautar Sarkin Fulani sai da izini gwamnati.
Ya ce akwai takarda a rubuce, domin ko a wajen bikin nadin sarautar akwai wasu masu manyan mukaman gwamnati da suka halarci nadin.
Ya yi kira ga kwamitinin da gwamna ya kafa da ya yi wa Sarkin ‘Yandoto adalci, sannan duk wanda ke da hannu a kai komai mukaminsa a hukunta shi, domin ba Sarkin ‘Yandoto kadai ba ne ke da hannu, akwai wasu sarakuna.
Sakamakon Allah wadai da al’ummar kasar nan suka yi saboda nadin kasurgumin dan ta’adda, Ado Aleru a matsayin Sarkin Fulani a karkashi masarautar Sarkin ‘Yandoto, gwamnatin Jihar Zamfara ta nesanta kanta da nadin.
Wannan yana dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Jihar zamfara, Kabiru Balarabe, wacce aka raba wa manema labarai a Gusau, Babbar birnin Jihar Zamfara.
Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa, Gwamna Bello Mohammed Matawalle, ya bayar da umarnin dakatar da Sarkin ‘Yandoto, Mai Martaba Aliyu Garba Marafa nan take. Kuma ya amince da nada kwamitin da zai binciki yadda abun ya kasance.
Wadanda aka nada a matsayin ‘yan kwamitin sun hada da Hon. Yahaya Chado Gora, a matsayin shugaba da Hon. Yahaya Mohd Kanoma da Hon. Muhammad Umar B/Magaji da Hon. Lawal Abubakar Zannah da Isa Muhammad Moriki da Barista Musa Garba.
Kuma a nan take gwamnatin ta bayyana Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin ‘Yandoto a matsayin wanda zai kula da harkokin masarautar.
…Ya Kashe Mutum 100 A Katsina, In Ji ‘Yansanda
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa har yanzu fitaccen dan Ta’adda Ado Aleru, wanda masarautar Yandoto Daji ta jihar Zamfara ta yi masa rawanin sarauta a ranar Alhamis din da ta gabata, har yanzun yana cikin jerin sunayen wanda take nema ido-rufe.
Rundunar ta ce Alero ya kashe mazauna jihar Katsina 100.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani kan sarautar da aka baiwa shugaban ‘yan bindigar a jihar Zamfara.
Isah ya ce rundunar na tuhumar Aleru d
a laifukan da suka hada da kisan kai, ta’addanci, fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Ya kara da cewa, ana kuma neman Aleru da laifin kashe mutane sama da 100 a kauyen Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a jihar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a watan Yunin shekarar da ta gabata na neman Alero mai shekaru 47 da haihuwa a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, ruwa a jallo, inda ta daura kyautar Naira miliyan 5 – a mace ko a raye ga duk wanda ya kawo mata shi.