Dashishi na daya daga cikin abincin da ake marmarinsa sosai musamman a kasarmu ta Hausa. A baya, dashishi abinci ne na sarakuna da manyan hamshakai, amma a halin yanzu, Alhamdu Lillah talakawa ma suna iya yi.
Da farko zaki samu alkamar ki sai ki wanke ta sosai ki fitar da dukkan harkakinta sannan ki tabbatar kin gere tsakuwar ciki. Daga nan sai ki ba da a surfa maki ita watau a cire maki dusar alkamar. Bayan an dawo miki da ita sai ki bakace, ki wanke ki sake shanyawa. Idan ta bushe sai ki bayar a barza maki ita da kyau, sai ki kunna wuta ki dora, idan ta dafu sai ki sauke a zuba wa maigida da sauran iyalai. Ana iya ci da duk miyar da kike so.