Jiya Jumma’a 31 ga watan Mayu, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da wasu baki daga kasashen Larabawa, da suka zo kasar Sin don halartar taron ministoci karo na 10, na dandalin tattauna hadin-kan kasar Sin da kasashen Larabawa.
A yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Somaliya, Ahmed Moallim Fiqi, minista Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Somaliya sosai, wajen kiyaye mulkin kai da cikakken yankin ta, kana tana mara mata baya kan kokarin da take yi na tabbatar da zaman karko a fannin siyasa, da inganta samar da tsaro, da kuma aiwatar da manufofin sake raya tattalin arziki. Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, a wasu muhimman fannoni, ciki har da aikin gona, da kamun kifi, da kiwon lafiya da dai sauransu, da kuma sa kaimi ga aiwatar da jerin shawarwarin kasa da kasa da kasar Sin ta gabatar, kamar raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” a kasar Somaliya.
- Tsarin Kiwon Lafiyar Yaran Kasar Sin Na Kara Kyautata, In Ji Jami’ar Hukumar Lafiyar Kasar
- Hakkin Bil Adam Iri Na Amurka Matakin Gatanci Da Babakere Ne
A nasa bangaren, minista Fiqi ya bayyana cewa, kasar Sin ta zama ma’auni, kuma fitila ga kasashe masu tasowa. Somaliya na fatan kara yin hadin gwiwa tare da Sin a fannonin samar da ababen more rayuwa, da makamashi, da zuba jari, da kiwon lafiya, da tsaro, da dai sauransu, a karkashin tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, da na Sin da kasashen Larabawa.
A yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Comoros, Dhoihir Dhoulkamal, minista Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwa tare da Comoros, a fannoni daban daban, wadanda suka shafi kawar da fatara, da ba da ilimi da horo, da kiwon lafiya da sauransu, da kuma kara shigo da kayayyaki masu inganci daga kasar Comoros.
A nasa bangaren, minista Dhoulkamal ya ce, kasarsa ta amince sosai da muhimmiyar shawarar da shugaba Xi Jinping ya gabatar, kan hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa. Kaza lika, ta nuna tsayayyen goyon baya ga bangaren Sin, wajen kiyaye cikakken yankin kasa. A cewar ministan, shawarar “Ziri daya da hanya daya”, tana taimaka wa kasashen Larabawa da na Afirka, wajen samun ci gaba tare, kuma kasar Comoros za ta ci gaba da himmatuwa wajen shiga cikinta. (Bilkisu Xin)