Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 ta yi nasarar sauka a wani yankin da aka zaba a gefen wata mai nisan gaske a ranar 2 ga Yuni, bayan da ta yi tafiyar kwanaki 30 zuwa duniyar wata, tun bayan da aka harba ta kuma ta shiga falaki a ranar 3 ga Mayu. Wannan wani mataki ne mai cike da tarihi a fannin aikin binciken sararin samaniya na kasar Sin da kuma yadda dan Adam ke amfani da sararin samaniya cikin lumana.
Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta zurfafa yin mu’amala da hadin gwiwa da kasashen duniya a sararin samaniya bisa tushen yin adalci da daidaito da moriyar juna, da yin amfani cikin lumana, da samun bunkasuwa tare, da raba nasarorin da aka samu tare da sauran kasashen duniya, da yin nazari kan sirrikan sararin samaniya tare. (Yahaya)