Ma’aikatar kula da albarkatu ta kasar Sin, ta ce kasar ta samu gagarumin nasara wajen karewa da kyautata muhallin halittu a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya bayar da gudunmuwa ga kokarin duniya na samar da alumma mai zaman jituwa tsakanin halittu da bil adama.
Wata jamiar maaikatar Lu Lihua ce ta bayyana haka a jiya, yayin wani taro da ofishin shirin kula da muhalli na MDD (UNEP) ya shirya, inda ta ce, yayin da take amfani da tsarin shata iyaka wajen ware yankuna masu rauni, kasar Sin ta kyautata kimanin kadada miliyan 6.7 na muhallin halittu da ya hada da tsaunuka da koguna da dazuka da gonaki da tabkuna da yankunan ciyayi da hamadu.
A nasa bangare, Tu Ruihe shugaban ofishin UNEP a kasar Sin, ya ce kasar ta samu yabo sosai daga kasa da kasa bisa kaddamarwa da samun nasara a aikin kyautata muhallin halittu mafi girma a duniya. Ya kuma bayyana fatan kasar Sin za ta yayata gogewarta ga sauran sassan duniya. (Mai fassara: Faiza Mustapha)