ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Na Hada Kai Da Kasa Da Kasa A Kokarin Inganta Muhallin Halittun Duniya

by CGTN Hausa
1 year ago
Sin

Lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin lardi ne da aka fi yawan samun kwal a kasar Sin. Sai dai yayin da ra’ayin nan na samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba ke kara zame wa al’ummar kasar jini da tsoka, a wannan yankin da Allah ya albarkace shi da kwal, ana ta samun sauye-sauye ta fannin nau’o’in makamashin da ake amfani da su.

Kauyen Zhuangshang wani karamin kauye ne da yawan mazaunansa bai wuce dubu ba, wanda in an duba, tamkar ba shi da bambanci da sauran kauyukan da ke arewacin kasar Sin, kawai in an lura, za a ga farantan samar da wutar lantarki ta hasken rana da aka kakkafa a rufin gidaje da ma filaye da dama na kauyen, farantan da suka samar da babban sauyi ga mazauna kauyen ta bangaren makamashi. Kowace rana da safe, da rana ta fito, to, farantan sun fara aiki ke nan, wadanda suke ta samar da wutar lantarki ga magidanta na wannan kauye, wadanda suke amfani da ita wajen dafa abinci da haskaka daki da ma sauran harkokin rayuwa, har da gudanar da ayyukan gona, matakin da ya sa mazauna kauyen suka kawo karshen yin amfani da kwal da ma sauran nau’o’in makamashi na gargajiya. Hakan kuma ya sa kauyen yin fice daga shirye-shirye sama da 2000 da aka gabatar a taron MDD kan sauyin yanayi karo na 28 da aka gudanar a bara, wanda har ya samu lambar yabo na “mai kawo sauyin fasalin makamashin da ake amfani da shi.”

  • Firaministan Pakistan: Dangantakar Da Ke Tsakanin Pakistan Da Sin Ba Za Ta Wargaje Ba
  • Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba A Bangaren Kyautata Muhallin Halittu

Abin da ya faru a kauyen Zhuangshang wani bangare ne kawai na ci gaban da kasar Sin ta samu wajen tabbatar da bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, fadin dazuzzukan da aka dasa a kasar Sin ya kasance na farko a duniya, kuma kasar ita ce kasar da dazuzzukanta suka fi saurin karuwa a duniya, karuwar da ta kai kimanin kaso 1/4 na duk duniya cikin shekaru kusan 20 da suka wuce. Baya ga haka, a bara, karuwar yawan wutar lantarki da ake samarwa ta rana da iska da ma sauran nau’o’in makamashi masu tsabta a kasar Sin ta ninka ta kasashen kungiyar G7 har sau hudu, ta kuma ninka ta sauran kasashen duniya gaba daya fiye da sau biyu. Duk wadannan abubuwa sun faru ne sakamakon yadda tunanin nan na “kyakkyawan muhalli shi ne kadarori masu kima” ke kara zame wa Sinawa jini da tsoka a rayuwarsu ta yau da kullum. A sakamakon tunanin, duniya ta shaida yadda kasar Sin ta yi ta kara kyautata, haka kuma ta samar da gudummawa ga kyautatar muhallin halittu na duniya baki daya.

ADVERTISEMENT

In mun dauki sabbin makamashi a misali, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta zamanto ta farko a duniya ta fannin samar da sabbin makamashi, don haka ma, ya zama wani muhimmin bangaren da kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. A yankin De Aar da ke tsakiyar kasar Afirka ta Kudu,na’urorin samar da wutar lantarki da karfin iska, suna samar da wutar lantarki sama da KW miliyan 750 a kowace shekara, kuma ta hakan an yi tsimin kwal kimanin tan sama da dubu 200, tare da rage fitar da iskar Carbon kimanin tan dubu 700. Sai kuma a yankin Garrisa na kasar Kenya, wani kamfanin kasar Sin ya kafa tashar samar da wutar lantarki da zafin rana irinta mafi girma a gabashin Afirka, wanda ya sassauta matsalar karancin wutar lantarki da kasar ta fuskanta, kuma ba tare da fitar da iskar Carbon ba. A kasar Nijeriya, kamfanin kera bas bas na Yutong na kasar Sin, ya samar da bas bas masu aiki da wutar lantarki a birnin Lagos, karon farko ke nan da kasar ta fara samun wannan sabon nau’in motocin bas.

A kokarin da kasar Sin ke yi, an kaddamar da jerin shirye-shirye na tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a dimbin kasashe masu tasowa, wadanda suka sa kaimi ga kyautatar muhallin halittun duniya.

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Yau ranar kiyaye muhallin duniya ce karo na 53, haka kuma zagayowar ranar kare muhalli ta 10 ce a kasar Sin.Duniyarmu gida na bai daya ne ga dukkanin dan Adam, kuma makomar dan Adam daya ce a fannin tinkarar matsalolin muhalli. A yayin da kasar Sin ke ci gaba da kokarin inganta muhallin halittu na cikin gida, za ta kuma ci gaba da samar da gudummawa, da hada hannu da sassan kasa da kasa, musamman ma kasashen Afirka, don kara inganta muhallin duniyarmu baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 4, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Ra'ayi Riga

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 4, 2025
Next Post
Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Nemi Al’umma Su Nemi Watan Zul-hijja Daga Gobe Alhamis 

Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Nemi Al'umma Su Nemi Watan Zul-hijja Daga Gobe Alhamis 

LABARAI MASU NASABA

APC

Sauya Sheƙa: Yadda APC Ke Ci Gaba Da Hamɓarar Da Jam’iyyun Adawa A Majalisa

November 11, 2025
An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia

An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia

November 11, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa

November 11, 2025
‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina

‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina

November 11, 2025
Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

November 11, 2025
HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano

HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Da ‘Yan Ta’adda Sun Fi Sojojin Nijeriya Yawan Makamai – Babachir

‘Yan Bindiga Da ‘Yan Ta’adda Sun Fi Sojojin Nijeriya Yawan Makamai – Babachir

November 11, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170

November 11, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn

November 11, 2025
Rashin Aiki Ga Matasa Babbar Barazana Ce Ga Nijeriya – Obasanjo 

Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.