Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa cikin watanni uku an haifi jarirai 27,490 a fadin jihar.
Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa babban daraktan hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano, Dakta Nasiru Alhasan Kabo, ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da shirin rarraba kayan kula da lafiya ga asibitocin kula da lafiya na matakin farko da na biyu da kuma na uku.
- Muna Da Irin Akidar NEPU Da PRP A Siyasarmu -Shugaban SDP
- Halin Da Ake Ciki A ‘Yandoton Daji Bayan Nadin Sarautar Dan Ta’adda
Dakta Nasiru ya ce kayan da aka raba da kudinsu ya kai Naira miliyan 15 na haihuwa ne da kayan bayar da na sashen kula da bayar da agajin gaggawa da na kula da yara.
Ya ce a cikin adadin, anyi tiyata ga mata masu ciki guda 681(CS), kuma irin magungunan da ake bayarwa suna taimakawa.
Sannan ya jinjinaw a abokan hulda saboda taimakon da suke bawa harkar lafiya a jihar.
Bugu da kari ya bukaci kungiyoyin fararen hula da su ci gaba da tallafa wa bangaren lafiya.