Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar, da shugaban jami’ar Kean ta Amurka, Lamont Repollet ya aika masa a kwanan baya, inda ya yi kira da a kara hadin gwiwar jami’o’in kasashen biyu, don taka rawar gani wajen gaggauta ingiza zumuncin kasashen.
Xi Jinping ya bayyana gamsuwa cewa, a shekarar 2006 a jami’ar Kean, ya ganewa idonsa kulla yarjejeniyar kafa jami’ar Wenzhou-Kean a birnin Wenzhou dake kasar Sin tsakanin kasashen biyu. Ya ce a yanzu kuma, ana samun ci gaba mai armashi karkashin hadin gwiwarsu, har makarantar ta zama abin misali ga hadin kan kasashen biyu a bangaren ba da ilmi.
Kazalika, Xi Jinping ya ce, huldar kasashen biyu na da alaka da zamantakewar jama’arsu da ma makomar Bil Adam baki daya. Ya ce hadin gwiwa a bangaren ba da ilmi na iya ingiza mu’ammalar jama’a musamman ma matasa. Yana mai bayyana hakan a matsayin wani mataki na hangen nesa wajen raya huldar kasashen biyu. Ya kara da cewa, yana farin ciki cewa, a cikin wasikarsa, Lamont Repollet ya bayyana fatansa na zurfafa hadin kan dalibansa da na jami’ar Wenzhou-Kean, da ma karawa dalibansa kwarin gwiwar kara ilmi a Sin. Yana mai fatan jami’o’in kasashen biyu za su kara tuntubar juna da hadin kai don horar da masanan dake nazarin harkokin kasashen biyu sosai, ta yadda za su kafa wata gada mai kyau tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)