Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya jaddada goyon baya da jajircewarsa na ci gaba da gudanar da ayyuka masu inganci a kananan hukumomi don ci gaban kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake mika sabbin motoci samfurin Toyota Hilus ga shugabannin kananan hukumomin jihar 11 a wani takaitaccen biki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gombe.
“Wadannan motocin ba na alfarma ba ne ko na jin dadi, na aiki ne. An samar da su ne don tallafa wa ayyukan kananan hukumominku, wadanda babban nauyin da ya rataya a wuyansu shi ne kula da jin dadi da walwalar jama’a daga tushe,” in ji shi.
- Liƙi Da Takardun Naira Ya Jefa Wata Mata Komar EFCC A Gombe
- Ƴansandan Gombe Sun Yi Ram Da Ɓarayin Hanyar Jirgin Ƙasa
Ya bukaci shugabannin su yi amfani da motocin wajen shiga kowane lungu da sako na kananan hukumominsu don inganta ayyuka ga al’ummarsu, yana mai ba da tabbacin ci gaba da sanya ido kan yadda ake amfani da motocin don tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Ya ce, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen sanya ido kan yadda kuke tafiyar da dukiyoyin al’ummarku da kuma yadda kuke aiwatar da ayyukan da ke da tasiri ga jama’arku”.
Ya kuma yi kira ga shugabannin da cewa su tashi tsaye wajen samar da kudaden shiga da kuma samar da ayyuka ga al’umma don dafa wa kokarin gwamnatin jihar a fagen samar da ci gaba. Gwamnan ya jaddada rawar da tsarin mulki ya bai wa kananan hukumomi a matsayinsu na mataki na uku na gwamnati.