A fadi-tashin da yake yi wajen samar da ingataccen tsaro, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar Jihar Zamfara.
A ranar Talatar nan ne gwamnan ya halarci bikin yaye wasu dakaru na musamman, wadanda ke karkarshin Hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ake kira ‘Agro Rangers’ a Jihar Zamfara.
- Sin Ta Kiyaye Zaman Lafiya Da Tsaron Kasa Da Kasa Bisa Ayyukanta Masu Amfani
- Sirrin Zaman Lafiyar Da Ake Mora A Jihar Nasarawa –Kakakin Gwamnan Jihar
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, dakarun na ‘Agro Rangers’, jami’ai ne na musamman a Hukumar ta Sibil Difens, wadanda suka samu horo mai zurfi.
Ya kuma kara da cewa, an horar da jami’an na musamman a shirye-shiryen gudanar da aikin hadin gwiwa a yaki da ’yan bindiga a Jihar Zamfara.
A yayin jawabinsa a wajen bikin, gwamna Lawal ya yaba wa hukumar NSCDC bisa wannan shiri nasu. Ya ce, “Wannan ya zo ne a wani muhimmin lokaci kuma ya yi daidai da kudurinmu na daukar ingantattun matakan yaki da rashin tsaro.
“Mun dauki wannan a matsayin babban mataki na tunkarar kalubalen da ya kawo cikas ga al’ummar mu wajen ayyukan noma, sana’o’in dogaro da kai, da sauran hanyoyin sa-mar da abinci a jihar.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana harkokin tsaro da noma a matsayin muhimman abubuwan da suka sa a gaba. Mun bullo da matakai daban-daban don magance kalu-balen tsaro da kuma bunkasa noma a jihar. Don haka, muna kallon wannan shiri na ja-mi’an Hukumar Sibil Difens a matsayin wani gagarumin mataki na ci gaba da daukar matakan tsaro da muke dauka a matsayin gwamnati tare da jami’an tsaro da ke aiki a jihar.
“A matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da bada hadin kai da cibiyoyi, kungiyoyi da daidaikun mutane wajen yaki da duk wani nau’in miyagun laifuka. Mun himmatu wajen samar da tallafin da wadannan cibiyoyi da daidaikun mutane ke bukata don gudanar da ayyukansu. Manufar farko ita ce tabbatar da tsaron al’ummominmu da kuma sanya su cikin aminci don ayyukan zamantakewa da tattalin arziki wanda zai saukake ci gaban jihar da jama’a.
“Ina matukar fatan shirin hukumar NSCDC na samar da wani dakarun na musamman, wanda hakan zai samar da mafita mai dorewa ga kalubalen tsaro da ake fuskanta, mu-samman wadanda suka shafi harkar noma.
“Ina da alfahari da kaddamar da wannan dakaru. Ina yi muku fatan alheri bisa sauke nauyin da aka dora muku. Ina rokon Allah Ya tsare ku, sannan Ya yi muku jagoranci.”
Tun da farko, Kwamandan Rundunar Sibil Difens a Jihar Zamfara, Kwamanda Sani Mustapha, ya gode wa Gwamna Lawal da gwamnatin Jihar bisa tallafin da suka ba shirin horarwa da dakarun Agro Rangers.
“Yallabai, dimbin goyon bayan da ka ke baiwa rundunar ta sa muka kai ga haka. Muna godiya kwarai da gaske,” inji shi.
Kwamandan ya kara da cewa, Hukumar ta NSCDC ta himmatu wajen samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice a yankunan da ake fama da rikici.