Ma’aikatan gwamnati a Nijeriya sun bukaci gwamnonin jihohi da su rage yawan albashi da alawus-alawus da na wadanda suka nada mukamai domin samun damar biyan sabon mafi karancin albashi na N62,000 da gwamnatin tarayya za ta gabatar.
Ma’aikatan da suka zanta da manema labarai a jiya, sun soki gwamnonin kan cewa ba za su iya biyan sabon albashin ba.
- Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Naira 62,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
- Karin Albashi Ya Zama Karfen Kafa A Nijeriya
Ma’aikatan sun ce za su kai karar gwamnoni idan sun ki aiwatar da sabon mafi karancin albashi idan gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Wannan shi ne matsayar da kungiyar kwadago a Nijeriya ta bayyana kan matakin gwamnonin jihohi kan sabon mafi karancin albashi a matsayin rashin tunani da mugunta da son kai.
Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, a ranar Juma’a, ta bayyana cewa gwamnatocin jihohi ba za su iya biyan Naira 60,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ba, kuma wasu jihohi za su koma karbar rance don biyan ma’aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp