Assalamu alaikum masu karatu barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku hada maganin kuzari yayin jima’i
Abubuwan da za a tanada:
Ganyen zogale, ‘ya’yan zogale, citta, kaninfari, masoro, kimba:
Yadda za ki hada:
Kowanne ana son a samu busasshe, sai ki hade su waje guda ki dake su, su yi laushi, za ki rika diban karamin cokali ki zuba a shayi mara madara, ya yi kamar sawon minti 15 saboda ya jiku sannan ki sha, safe da yamma.
Wannan fa’ida kuma tana maganin sanyin mara ciwon mara da mataccen maniyyi da amosanin mara.
Yadda za ki kara wa Maigida karfi
Na daya; A samu garin Habbatus sauda kofi daya, garin Zaitun kofi daya, garin Tafarnuwa rabin kofi sai Zuma kofi biyu. Sai a hada su waje daya, sai a dinga zuba cokali daya a shayi ba madara ana sha kullum sau daya, bayan an ci abinci.
Na biyu; A samu Alkama gwangwani hudu, garin Habbatus sauda kofi daya. Sai a gyara Alkamar, a nika ta, a hade su waje daya. Kullum a zuba cokali daya a rabin kofi na shayi ba madara a sha.
Na uku; A lazimci shan zuma cokali biyu a cikin ruwan dumi kullum.
Na hudu; A samu saiwar Burku da itacen Zumbur sai a hada su waje daya, kullum mai gida ya dinga sha sau biyu.
Na biyar; A samu danyen kwai kamar guda talatin. Kullum sai a dafa guda daya, sai ka cire kwanduwar, farin kwan kawai za ka ci tare da yankakkiyar albasa kullum ka ci daya har kwan ya kare.
Na shida; A samu gaban Ayu, sai a saka a cikin zuma har tsawon kwana bakwai. Idan ya jiku sai ka dinga lasar zumar har ka shanye.
Na bakwai; A samu Gurji da Ayaba, sai a markada a yi lemon juice a sa zuma maigida ya dinga sha.
Na takwas; A samu busasshen Muruci da garin Kashe-Zaki da Farin-Magani da Farin -Mauro. Sai a hada su waje daya a daka a tankade. Sai ka dinga zuba cokali daya a shayi ba madara kana sha kullum sau daya.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu