Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na shirin yin garambawul a majalisar ministocinsa, inda ake sa ran zai nada sabbin ministoci, da kuma samar da sababbin ma’aikatu da kuma yunkurin samar da ma’aikatar da za ta kula da kebe da kuma bunƙasa harkar kiwon dabbobi.
Wannan ma’aikatar dai za ta kasance a karkashin Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Majalisa Za Ta Karbi Ƙudurin Sabon Mafi Karancin Albashi – Tinubu
- Mun Fara Aiki Da ‘Yan Bori – Hukumar Tace – Fina-finai
Baya ga samar da wannan sabuwar ma’aikata, Tinubu na shirin nada kananun ministocin a ma’aikatu da ba su da ƙananan minista.
Ministocin da za a samar musu da ƙananan ministocin sun haɗa da na Ayyuka da Kwadago da Ma’aikatar Jin kai da Rage Talauci.
Sauran sun haɗa da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ma’aikatar Makamashi da Ma’aikatar Kula da Al’adu da Ɓunkasa Tarihi.
Sauye-sauyen ya biyo bayan tantance ayyukan ministoci da shugaba Tinubu ya yi.