Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da fara biyan sabon tsarin Albashi na Naira dubu Talatin daga dubu Shida a Yau na wannan watan da muke ciki don ma’aikata suyi hidar Sallah cikin walwala.
Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a wajan taron ranar Dimokaraɗiyya a yau a filin dandalin ƴanci da ke tsakiyar garin Gusau, Babban birnin Jihar Zamfara.
- Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara
- Sin Ta Samu Nasarar Zama Mamba A Kwamitin Gwamnatocin Dake Kula Da Kiyaye Kayayyakin Al’adu Marasa Ganuwa
“A Jawabin nasa gwamna Dauda ya ɗau alwashin inganta iin daɗin ma’aikata wanda abin takaicin ne tsawon shekaru da Gwamnonin da aka yi suka shuɗe a Zamfara sun gaza biyan ma’aikata tsarin albashi mafi ƙaranci na dubu Talatin sai na dubu shida.
A kan haka ne ya tabbatar da cewa, yau cikin daren nan In sha Allah kowane ma’aikaci zai ji albashinsa na wannan wata kuma sabon tsari inji gwamna Dauda.