“Na shiga wani hali sosai dan suma na rika yi, ‘yan gidanmu suna watsa mun ruwa ina farfadowa….” Kadan daga cikin kashi na biyu na tattaunawar da wakiliyarmu, RABI’AT SIDI BALA ta yi da tsohuwar matar Adam A. Zango kuma fitacciyar jarumar da ke taka rawa a yanzu cikin shiri mai dogon zango na Labarina a masana’antar Kannywood wato, AMINA UBA HASSAN, ke nan. Ga karashen tattaunawar kamar haka:
Mene ne ba za ki taba mantawa ba game da Adam A. Zango na dadi da na daci?
Eh! To, akwai abubuwa da yawa da ba zan manta da su ba, misali kamar; Irin son da ya nuna mun kafin ya aure ni har ya aure ni, da kuma kullen da ya nuna man ko bayan rabuwarmu, dan ina daya daga cikin matan Adamu da take kiran wayarsa kai tsaye, ko kuma idan yana wuri zan iya zuwa na same shi mu gaisa in ya ganni a guri zai tsaya mu gaisa za mu yi wasa da dariya to, abubuwa na dadi da ba zan manta da shi ba sunada yawa.
- Kalau Nake Babu Abin Da Ke Damun Kwakwalwata – Adam Zango
- Abin Da Ya Sa Nake Rungumar Ɗana Ina Wakar Soyayya – Tsohuwar Matar Adam Zango, Amina
Dan daya daga ciki ma zan iya cewa abubuwan girki ya koya mun wasu abubuwan a zaman aurenmu dan ya aure ni ina ‘yar karama na gama ‘Secondary School’, kuma a gida komai yi maka ake yi ba abin da ka ke yi, amma bayan ya aure ni ya koya mun wasu abubuwa dan shi ya iya girki, iya nawa shi ne; gyara gidana, ko ina tsaf-tsaf, na feffesa turare duk na iya wannan in yi wanka in yi kwalliya amma akwai abubuwa da yawa da ba za su kirgu ba na jin dadi da ba zan iya mantawa da Adamu a kan shi ba. Mara dadi kuma ‘I can’t see’ yanzu ba ma tare ba wani abu da zai iya yi mun ko na rashin dadi tunda ba wai muna tare bane.
Kin san an ce idan alkhairi ‘sometimes’ in mutum ya yi maka abu ka rika aunawa wanne ya fi yawa Alkhairin ko sharrin? To, alkhairin jin dadin ya fi rashin jin dadin yawa shi ya sa ban da wani abu na rashin dadi da zan fada gaskiya.
Misali a ce yaronki yana son shiga harkar fim, shin za ki amince ya shiga ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan a kan yaranki?
Idan dai har alkhairi ne ai sana’a ce ita ce mahaifinshi yake yi, ita ta mayar da shi abin da ya zama a yau, da kudin harkar fim aka auri uwarsa, da kudin harkar fim ake kula da shi tun yana karami har ya kai yanzu to, idan ya ce yana so iyaka a matsayina na mahaifiyarsa sai dai na bashi shawara na bi shi da addu’a, idan a san kaina ne ina son ya zama ‘Airpost officer’, ina so ya zama watarana, idan kuma fim yake ao yayi iya ka na bashi shawara na bishi da addu’a.
Idan mahaifinshi baya bukatar hakan a gare shi, shin za ki amince da maganar mahaifinshi, ko kuwa za ki goyi bayan danki?
Mahaifinshi ne, ai ba zai so yayi abin da zai bata rayuwarsa ba, abu ne na shawara, abu ne wanda ya zama dole ni da shi kuma daya shafi danmu mu tsaya mu yi shawara, dole zai ban dalilansa ni ma na ba shi dalilai na, idan na shi ya fi nawa falillahil hamd, idan kuma nawa ya fi nashi falillahil hamd, a karshe dai idan aka tsaya aka yi magana ta hankali dole dai zai zama an tsaya a matsaya guda.
Mu koma can baya, ya ki ka dauki fim a wajenki?
Na dauki fim sana’a, na biyu kuma ‘fashion’, saboda abu ne da nake yi nake kuma jin dadin yin sa.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta bayan shigarki cikin masana’antar Kannywood?
Gaskiya babu wani kalubale dana taba fuskanta har zuwa yanzu, ban san dai gaba ba tunda ba a fata.
Wadznne irin Nasarori ki ka samu game da fim?
Nasarori gaskiya ba a iya kirga su, nasarori sosai fiye da tunani, na samu nasarori sosai ina ma kan samu, kuma ina fatan na ci gaba da samu in sha Allah.
Mene ne burinki na gaba game da harkar fim?
Burina nan gaba shi ne; Yau koda a ce nayi aure ya zama ina so na ga ina daraktin din fim ko da aure na. Wanda zan aure mutum ne wanda bai da matsala da koda nayi auren na ci gaba da fim dina, tunda sana’a ce, na dauke ita sana’a kuma zan rike mutuncin aure na to, amma ni dai ban fatan hakan, na fi so idan nayi auren nayi shi kenan.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka, wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba?
Ranar da dana ya sauke alkur’ani mai girma, yana daga cikin ranakun da ba zan taba mntawa ba, a ce yau yaron dana haifa a cikina na shayar ya sauke alkur’ani, ita ce ranar farin cikin da ba zan manta da shi ba. Na bakin ciki kuma shi ne ranar da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne ranar da aka kwace Haider a hannuna na shiga wani hali sosai, dan suma na rika yi, ‘yan gidanmu suna watsa mun ruwa ina farfado wa, ina fita sai dai a dauko a dawo da ni cikin gida, na zama kamar wata mara hankali, saboda ba wai na san da za a karbe shi bane, kawai daga ya je yaho da babanshi ya dawo sai sakon babanshi na gani cewar ya rike Haider nayi hakuri.
Wannan ranar yana daya daga ranakun bakin cikin da na ji kamar na kashe kaina ma, sai kuma rasa iyayena guda biyu da nayi, na rasa mahaifiyata da farko ya zamana ba mu da wani gata daya wuce kakar mu, ita ta zama kamar Uwa ta zama Uba a gurinmu, ko babanmu yana nan ko baya nan ita ma ta zo ta rasu, sai daga baya Allah ya dauki ran mahaifina, ba zan taba mantawa da wannan ba a rayuwata.
Wace ce babbar kawarki cikin masana’antar kannywood?
Ba ni da babbar kawa a cikin masana’antar kannywood.
Bayan sana’ar fim kina wata sana’ar ne ko kuwa iya fim ki ka tsaya?
Kafin na fara fim inada shago ina shaloon, da turaruka da sauransu, kafin na fara fim ban saki shagon ba ina ‘planning’ wani abu akwai wani dan’uwana da yake ajjiya cikin shagon kowane shekara yana biya, akwai abin da nake.
Ya ki ke iya hada karatunki da kuma sana’ar fim, musamman yadda za ku bar gari domin daukar fim, shin hakan baya shafar karatunki ko ya abin ya ke?
Gaskiya yana shafa sosai duk da dai ni Alhamdulillah da akwai idon duniya in kana so ka ban tashin hankali ka ce mun karatu, bana shiri da karatu bana shiri da boko, kawai muna yinta ne saboda kwalin kawai muke bukata muna ganin gobe zai iya yi maka amfani ko ba ta gurin samun aiki ba zai iya yi maka amfani,
Me za ki ce ga masu kokarin shiga cikin masana’ar kannywood?
Kowa da sa’arsa yake zuwa, iya ka na ce su dauka sana’a suke yi kar su dauke shi kawai a ganni a TB, su yi shi da soyayya, su dauke shi sana’a sosai. Idan suka dauke shi sana’a to, shi ma zai dauke su ‘actors’.
Wane sako ki ke da shi ga masu kallo da kuma masoyanki?
Ni masoyana ba abin da zan iya fada musu na nuna musu ‘how appreciate like’ dadin yadda nake jin dadin kaunar da suke nuna mun, ba abin da zan ce musu sai dai kawai na ce Allah ya saka musu da alkhairi kuma su ci gaba dan yanzu aka fara, ina so na gode musu dan godiya ‘to me isn’t enough’ kamar yayi kadan saboda irin son da suke nuna mun, sai dai na ce na gode Allah ya saka musu da alkhairi.
Misali wani cikin masana’antar kannywood ya nuna yana sonki kuma zai aure ki, shin za ki amince da hakan ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan?
Gaskiya ba zai ma iya faruwa ba, ba ni da ra’ayin haka, auren wani dan kannywood ban ma sa shi ma cikin ‘calculation’ din rayuwata ba, wancan dai Allah ya yi za a yi kuma an yi, amma ba za a kara ba, ban da wannan ra’ayin, ban ma taba tunaninshi ba, dan ba abu ne da zai yu ba.
Me za ki ce da masu karanta wannan hirar taki?
Muna godiya da karanta hirarmu da suke yi ‘because’ wani lokacin ta nan ne wasu suke sanin wane ne jarumin da suke so ko ba sa so.
Ko kina da waɗanda za ki gaisar?
Wanda zan gaisar ba za su wuce masoyana ba, masu nuna mun soyayya wasu ma da ban san su ba, ba su taba ganina ba, wasu ba su sanni ba, ba su san ya nake a zahiri ba, amma duk da haka suke so na, su kadai zan gaisar in ce musu duk ina gaishe su kuma ina godiya.