Gwamnatin Tarayya ta musanta rade-radin da ake na cewar ta sauya sunan titin tsohon shugaban Nijeriya na mulkin soji da sunan Wole Soyinka a Abuja.
A wata sanarwa da ta fitar a yammacin Litinin, mai dauke da sa hannun Rabi’u Ibrahim, mataimaka wa ministan yada labarai, ta karyata batun.
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Sama Da 80 A KatsinaÂ
- Masarautar Argungu Da Al’adunta (3) Bikin Kamun Kifi
“Bamu ta taba tunanin sauya sunan hanyar Murtala Muhammed da ke Abuja zuwa wani suna ba.”
Sanarwar dai na zuwa ne don magance da kuma karyata batun da ake yi na cewa gwamnatin tarayya na shirin sauya sunan Murtala Muhammad Way zuwa sunan fittacen malamin nan, Wale Soyinka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “Lokacin da za a kaddamar da sabuwar babban Hanyar kudancin birnin Abuja da ta hade da titin Murtala Muhammad, shi ne ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da shawarar sanya hanyar sunan Wale Soyinka.
“Sabuwar hanyar da aka sanyawa suna ta taso ne daga yankin Katampe zuwa Jahi, wanda ya hada da babbar hanyar Abuja ta Kubwa, kuma ta sha banban da titin Murtala Muhammed.”