Ma’aikatar kudin kasar Sin gami da ma’aikatar kula da harkokin ruwa ta kasar, sun ware kudin da yawansa ya kai Yuan miliyan 916, a wani kokari na tinkarar bala’in ambaliyar ruwa dake addabar yankunan kudancin kasar, gami da bala’in fari dake addabar arewacin kasar.
Daga cikin kudin, an ware Yuan miliyan 499, don tallafawa lardunan Guangdong, da Fujian, da Guangxi, da Guizhou, da Yunnan, da Zhejiang, da Hunan, da Hubei yakar bala’in ambaliyar ruwa, yayin da aka ware Yuan miliyan 417 don yaki da bala’in fari a wasu lardunan kasar Sin, ciki har da Hebei, da Shanxi, da Jiangsu, da Anhui da Shandong, da Henan, da Shaanxi da Gansu. (Murtala Zhang)