Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya sanar a yau Juma’a cewa, firaministan kasar Sin Li Qiang zai halarci taron shekara-shekara na Davos na lokacin zafi wato Summer Davos karo na 15 a birnin Dalian da ke arewa maso gabashin kasar. Kakakin ya ce, firaministan kasar Li Qiang zai gabatar da jawabi na musamman a wajen taron, inda zai gana da shugaban zartaswar dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya Klaus Schwab da kuma baki na kasashen waje, kuma zai yi tattaunawa da wakilan ‘yan kasuwa na kasashen waje.
Shugaban kasar Poland Andrzej Duda da firaministan kasar Vietnam Pham Minh Chinh za su halarci taron. Lin ya kara da cewa, sama da wakilai 1,600 da suka hada da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malamai masana, da manema labarai na kasashe da yankuna kusan 80 ne za su halarci taron. (Yahaya)