Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi shagulgulan sallah, duba da yanayin da aka yi bikin babbar sallah ta bana, wanda dalilin hakan ya sa muka ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wanna batu; Ko ya bikin sallah ya kasance a garuruwanku?, wane bambanci sallar Bara da ta Bana take da shi?, wadanne gurare aka kai ziyara a wannan sallar?. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jahar Jigawa:
To batun shagalin sallah sai dai mu ce Alhamdullilah tunda mun gudanar da sallah lafiya lau cikin nishadi da kwanciyar hankali, duk da akwai tarin matsaloli da suka addabi al’umma a wannan bikin sallah duba da yadda ake fama da tsadar rayuwa dama tsananin talauci a tsakanin al’umma. To magana ta gaskiya akwai bambanci sosai a tsakanin sallar bara da ta bana, kama daga samun damar siyan abun layya dama shidimar bikin sallah duba da yadda matsalar tsadar rayuwa, hauhawar farashi dama tsananin talauci ya addabi al’umma a wannan shekara,sai dai kawai mu yi addu’ar Allah ya karbi ibadar mu.
To magana ta gaskiya an ziyarci gidajen ‘yan’uwa domin gaisawa da kuma sada zumunci, sannan kuma mun hadu a majalisa domin gaisawa da kuma ciye-ciye da ‘yan’uwa da abokan arziki.
To abubuwan suna da dama amma wanda ya fi shi ne yadda al’umma suka gudanar da bikin sallah cikin nishadi da kwanciyar hankali duk da yanayi da’ake ciki na tsadar rayuwa dama tsananin talauci amma al’umma sun yi shidimar sallah daidai gwargwado.
To sakona na farko shi ne ina mika sakon barka da sallah ga dukkanin al’ummar musulmi na duniya Allah ya karbi ibadar mu, sai kuma ina kira ga masu hannu da shuni daya kamata su taimakawa masu karamin karfi a irin wannan lokaci na bikin sallah domin su na gudanar da bikin sallah cikin nishadi da kwanciyar hankali daga karshe nake addu’ar Allah ya karbi ibadar mu.
Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Kaduna:
Sallar bana Alhamdulillahi an gudanar da shagulgula kamar yadda aka saba, sai dai duba da yanayin rayuwa a nan jihar Kaduna an gudanar da shi ne gwargwadon iko. Ta bangararen ci ma kuwa, kayan sun zabure sai dai akai ta sarrafa shinkafar ‘Jollof’ ko ‘fried rice’. Tsadar rayuwa ita ce ta bambanta sallar bana da ta bara to amma duk da haka mutane sun yi kokari an ci an sha, an sanya tufafi kuma an samu walwala da nishadi.
Na dan kai ziyara a wannan sallar, na je gamji park na nan Kaduna. Sannan na ketare zuwa Katsina gurin yayata na kai mata ziyara na kuma yi kallon hawan sallah.
Babban abun da ya sani farinciki a wannan sallar shi ne kamar koyaushe na ga dandazon mutane a filin idi, mun gudanar da sallar idi cikin jin dadi an kuma yi ma kasa baki daya addu’a, an gaggaisa da taya al’ummar musulmai murnar zagayowar babbar sallah. Sakona ga sauran al’umma shi ne ina yi masu barka da sallah, Allah ya kara mana lafiya da zama lafiya. Allah ya sa mu gama lafiya.
Sunana Sa’idu Suleman Malam Madori A JIhar Jigawa:
Batun shagalin sallah an gudanar da shi cikin koshin lafiya anan Sabaru Kawaji Kano sai dai mu ce Alhamdulillah, mun gudanar da sallar Idi misalin karfe 9:00am a babban masallaci na Dakata Kawaji cikin aminci da hamdala,duk da kasancewar yanayin tsadar rayuwa da talauci a wannan lokaci. Anan akwai bambanci tsakanin sallar bara da kuma ta bana kasancewar yanayin tsadar rayuwa wanda ya haddasa karancin sayan abin layya har ma da shagulgulan bikin sallar baki daya, kawai sai dai hamdala kasancewar mu cikin koshin lafiya da kuma kwanciyar hankali tare da fatan Allah ya karbi ibadun mu. Kasancewar zumunci ginshikin arziki na ziyarci gidajen ‘yan’uwa da abokan arzuka dake kusa na nesa kuma an sada zumunci ta wayar salula domin kara dankon shi zumuncin.
Abin da ya bani sha’awa shi ne yanda al’ummah ke gudanar da bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali duk da yanayin tsadar rayuwa da muke ciki al’ummah sun fito ana hidindumu daidai gwargwado, ba abin da za mu cewa Allah sai godiya. Sako na shi ne ina mai mika sakon barka da sallah ga ‘yan’uwa da abokan arziki musamman iyaye da ‘yan’uwa kamar dan’uwa Aminu Adamu Mallam-Maduri, Sani Babangida, shuwagabannin mu kamar su mai martaba Sarkin kano da na Hadejia har ma da sauran al’ummah ta musulmi na duniya baki daya fatan Allah ya karbi ibadun mu baki daya.
Sunana Aisha D. Sulaiman:
Alhamdulillah an yi shagulgula na bikin sallah kowa cikin nishadi, sannan bambancin sallar bara da ta bana shi ne; bara rayuwa akwai sauki, amma bana babu sauki, bara an samu an yi yanka, bana kuma gaskiya masu yin saniya da raguna ma wani saniya ya samu wani kuma raguna gashi nan dai, wanda yake yin rakuma da tunkiyoyi kuma gaskiya wani ya samu daya ko biyu wani bai ma samu ba. Ga yanayin tsadar abinci ga yanayin kuncin da talaka yake ciki duk da dai me kudin ma ya taba yana cikin wani hali, ya kamata gwamnati ta dube mu ‘yan’uwa musulmi mu dage mu gyara halayenmu, mu dage da addu’a, wannan tsanani da muke ciki Allah ya kawo mana sassauci ya kawo mana dauki. Abin da ya fi burge ni shi ne yanayin yadda ake zuwa kai ziyara da sauransu duk da dai wannan sallar ba ta yawo bace.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Neja:
Shagulgulan sallah ni dai a bangarenmu yadda ya kasance sai dai mu ce Alhamdulillah, kamar yadda yake kullum haka yake, saboda duk abin da Allah ya nufa babu abin da za ka ce sai godiya. Mu kam Alhamdulillah yadda ta zaba wanzuwa haka take wanzuwa a ko’ina. Gaskiya ni dai ban ga bambanci ba a inda nake yadda take haka take bambancin daya ne Alhamdulillah, sai dai ban kai ziyara kowane gida ba irin na yahon sallah dan ni ba ma’abociya ce yaho bace ba, da ma a kno nake da mun yi ziyarce-ziyarce.
Sunana Muhammad Isah zareku Miga LGA, Jihar Jigawa:
Hausawa na cewa sallah biki daya rana daya tafi ce ta bar wawa da bashi, Salla ibada ce da addinin Musulunci ya sunnanta, wadda duk shekara ake yinta sau biyu wato karama da babba. A kan yinta kuma daga baya bukukuwa su shigo akan yi kwana hudu a garin mu ana bikin sallah.
Ana yin dinkin sabbin kaya da kuma ziyarar gidan ‘yan’uwa da abokan arziki, idi ranar sallah, tanadin kayan miya, girkin ranar salla, yanka ragon layya da sauransu. Sallar bana gaskiya sai a hankali saboda ta zo a tsadar rayuwa, layyar ma ba kowa bane zai iya yinta ba saboda matsin tattalin arziki na jama’a ke fama da shi. Gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki nake kaiwa ziyarar sallah. Abun da yake ban mamaki shi ne mafi akasarin mutane sai na ga basu samu damar yin sabbin kaya ba saboda tsadar rayuwa musamman yanka layya, ba kowa ne yake yinta ba. Sakon da nake da shi shi ne mu dage da yin addu’a akan matsin tsadar rayuwa, Allah ya kawo mana mafita.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Daga Jihar Katsina:
Mun gudanar da shagalin bikin sallah a jihar Katsina cikin farinciki da jin dadi kamar koyaushe, duk da cewar akwai bambanci tsakanin sallar bara da ta bana duba da yanayin tsadar rayuwa sai dai akai abun da za a iya. Amma duk da hakan Alhamdulillahi tunda akwai karar da ko mara shi na shaida ranar sallar ce dalilin kyautatawar da suke samu a wajen masu da shi, su nama da abinci da dan kwalam da makulashe. Na dan kewaya na yi ziyara cikin birnin Katsina tare da kanwata da mukai shagalin sallar tare cikin nishadi. Babban abun da ya sani farinciki shi ne yadda akai ta karakaina da ragunan layya ta ko’ina kamshi soye na tashi. Ka ci suya mabambamta gwanin dadi. Sako na ga sauran al’ummar duniya shi ne ina mana fatan rayuwa mai sauki, Allah ya warware mana wannan tsanani na rayuwa da jama’a ke fuskanta. Sannan Allah ya karo mana zaman lafiya da tsaro a jihata ta Katsina da kasa baki daya amin, Allah ya sa mu gama lafiya.
Sunana Usman Adamu Malam Madori A Jigawa:
Alhamdullilah Ma sha Allah yadda bikin sallah ya kasance anan garin mu wato karamar hukumar mallam-madori Jihar Jigawa, mun tashi da safiya mun yi wanka mun sa sabon kaya mun yi ado sosai da abokan arziki da kanne da yayu an hadu an je an yi sallah lafiya ma sha Allah, Allah mun gode maka. Maganar bambanci akwaita duba da yanayin yanka wato layya a kimanin mutun dari da suke layya bana bai fi mutun talatin bane suka yi, Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi Amun. Guraran dana kai ziyara sune kamar haka; Yayana Nasiru Adamu Aminu Adamu Malam Maduri, Anti faty, Malam Ibrahim mai shayi bakin falki. Ba komai bane ya sa mu farin ciki da annushuwa a wannan sallar kamar yadda na ga abokai da ‘yan’uwa an hadu an tafi masallaci tare abun ya burge ni na ji dadi. Ina yi wa kowa da kowa barka da sallah Allah ya maimaita mana Amin.
Sunana Maryam Abdullahi Wadata daga Jihar Kano:
Da farko dai shagulgulan sallah a garinmu ya kasance an aiwatar da shi cike da nishadantarwa da kuma lumana, a gaskiya ba wani bambanci tsakanin sallar bana da ta bara don za ma ace sallar bana ta fi ta bara kayatarwa. Duk da cewar mutane suna cewa ba a ziyara da babbar sallah amma ni na ziyarci ‘yan’uwa da kuma abokan arziki na kusa da na nesan musamman ta hanyar kiran waya dan shi zumunci ba lallai sai ta zuwa da kafa ba. Gaskiya abun da ya bada mamaki shi ne yadda a ka ga mai girma sarki Sunusi ya fito ya yi hawa duk da cewar jami’an tsaro sun hana amma hakan bai dakatar da shi da yin hawan ba. Ina mika sakon barka da sallah ga daukacin jama’ar musulmi na fadin duniya da fatan sun yi sallah lafiya, Amin.